
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani jirgin Kamfanin British Airways da ya taso daga Landon zuwa Abuja ya sauya sheƙa cikin gaggawa inda ya sauka a Birnin Barcelona da ke Ƙasar Sifaniya sakamakon rasuwar wani tsohon sojan sama daga Jihar Anambra ana tsaka da tafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a safiyar yau Litinin bayan bar Filin jiragen sama na Heathrow da misalin ƙarfe 11 na dare a jiya Lahadi da nufin isa filin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 5 na safiyar yau.
Al’amarin rasuwar tsohon soja ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare, lamarin da ya tilasta wa jirgin sauka a filin El Prat da ke Barcelona.
A cewar majiyoyi daga filin jiragen sama da iyalai, mamacin ya rasu ne yana da shekaru 80 da ɗoriya bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci.
An ruwaito cewa, yana ɗaya daga cikin sojojin da suka yi ritaya na Anambra da suke raye gabanin al’amarin.
Rashinsa ya jefa iyalansa da tawagar sojoji cikin jimami.
