Hukumar kiyaye haɗurra (KASSROTA)a Katsina ta gudanar da wani muhimmin zama tare da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan hanyoyin magance matsalar da ake fuskanta ta manyan motoci da ke ɗaukar dabbobi da mutane a lokaci guda a Katsina zuwa sassa daban daban na ƙasar.
Zaman wanda aka gudanar a babban ofishin hukumar da ke Katsina ya samu halartar wakilai daga jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
A yayin taron, babban daraktan hukumar KASSROTA Manjo Yahaya Rimi mai ritaya ya bayyana cewa wannan matsala ta daɗe tana jawo haɗurra da asarar rayuka, tare da haifar da barazana ga lafiyar jama’a.
Ya ce, motoci masu ɗaukar dabbobi da mutane a lokaci guda suna karya dokokin zirga-zirga manyan hanyoyin kasa.
Manjo Rimi ya ƙara da cewa hukumar ta ƙuduri aniyar daƙile wannan ɗabi’a ta hanyar sanya idanu a kan motocin dakon dabbobi, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin tabbatar da kowace mota ta bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa.
Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba da wannan mataki, inda suka bayar da shawarwari daban-daban kan hanyoyin magance matsalar.
Sun buƙaci hukumar da ta ci gaba da wayar da kan jama’a musamman direbobi da masu safarar dabbobi, tare da samar da tashar manyan motoci na musamman don jigilar dabbobi a cikin gari da wajen gari.
Taron ya cimma matsaya na kafa kwamitin haɗin gwiwa da zai kula da aiwatar da shawarwarin da aka cimma, tare da fara aikin wayar da kai da kuma hukunta masu karya doka nan bada jimawa ba.
Haka kuma wasu mutanen cikin garin Katsina sun koka kan yadda manyan motoci ke kashe mutane musamman ƙananan yara a cikin garin.
Kan haka an yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta hana mayan motoci shiga cikin gari kamar yadda wasu jihohi tuni suka ɗauki irin wannan mataki.
