Fitaccen malamin addinin Musulunci na Kano, Malam Na-Madabo ya rasu yana da Shekaru 80

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Fitaccen malamin addinin Musulunci daga unguwar Madabo a Kano, Malam Kabiru, ya rasu.

Majiyoyin daga iyalinsa sun bayyana cewa malamin ya rasu ne da yammacin ranar Alhamis bayan gajeruwar rashin lafiya, kuma rasu yana da shekaru 80 a duniya.

A cewar iyalan, za a gudanar da sallar jana’izarsa a ranar Juma’a da ƙarfe 10:00 na safe a Ƙofar Kudu ta gidan Sarkin Kano.

Sannan har ya zuwa lokacin rasuwarsa, Malam Kabiru ya kasance sananne a fannin ilimin addinin Musulunci mai zurfi, wanda ya ɗauki shekaru masu yawa yana koyarwa.

Kazalika ya shahara wajen ba da shawara ga ɗalibai, da kuma yaɗa ilimin addini a cikin al’ummar Madabo da ke ƙaramar hukumar Dala, da ma jihar Kano baki ɗaya.

By ukarofi