‘Yan sanda a Katsina sun kashe ‘yan bindiga biyar da kuɓutar da mutane 80

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan ƴan sanda CP Bello Shehu ya shaidawa manema labarai a ofishin sa lokacin da yake bayani kan nasarorin da rundunar yan sandan ta samu a watan da ya gabata.

Haka kuma kwamishinan ya sanar da kama mutanen 168 da ake zargi da aikata laifuka daban daban a faɗin jihar.

Laifukan sun haɗa da aikata fashi da makami,kisan kai,fyaɗe,lalata da satar wayoyin wutan lantarki na KEDCO mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba.

Akwai kuma waɗanda aka kama ɗauke da miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi.

CP Bello Shehu ya bayyana wasu daga cikin kayayyakin da aka kama waɗanda ake zargi mallakar waɗannan miyagun mutane ne.

Cikin su kamar yadda ya faɗa akwai bindagogi ƙirar AK 47 guda biyu da wata bindigar ƙirar gida tare da albarusai fiye da dubu ɗaya.

Kwamishinan yan sandan ya ƙara da cewa sun kuma gano motoci guda biyar da baburan hawa guda biyar duka da ake zargin cikin waɗanda aka kama ana zargin suna amfani da Kayan wajan aikata fashi da makami.

Haka kuma ‘yan sanda su gana ƙananan kwalebanin maganin tarin nan mai sa maye, TRAMADOL guda 1138 da tabar wiwi, harda wayoyin wutan lantarki.

CP Bello ya yaba da irin taimako da gwamnatin jihar gami da haɗin kan alummar jihar Katsina ke ba rundunar yan sandan da ya ce idan da ba irin wannan gudummawar da jami’an yan sandan ba su kai ga samun wannan gagarumin nasara ba.

Sai yayi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da da jami’an yan sandan haɗin kai wajan ƙoƙarin ɗauke da kakkaɓe ɓata gari da kawo zaman lafiya a jihar.

By ukarofi