Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano (KIRS), Dakta Zaid Abubakar, ya bayyana cewa babu wani cin karo da juna ko saɓani tsakanin dokokin haraji na hukumar da na Hukumar Tattara Haraji ta Tarayya (FIRS).
Dakta Abubakar ya ce duka hukumomin biyu masu tara kuɗaɗen shiga ne da ke aiki a ƙarƙashin tsarin haraji na ƙasa ɗaya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin taron tattaunawar masu ruwa da tsaki kan gyaran tsarin haraji da aka gudanar a Kano ranar Litinin, inda Daraktan Bin Doka da Tilasta Aiwatarwa na KIRS, Muhammad Aliyu, ya wakilce shi.
A cewarsa, “babu wani cikin karo da juna a dokokin haraji na tarayya da na jihohi. An tsara biyan haraji ne ta yadda masu biyan haraji za su san inda ya dace su biya kowane nau’i na haraji.”
Game da taron masu ruwa da tsaki, shugaban KIRS ya ce shirin, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar Agile Goɓernance and Climate Engagement (PACE), yana da nufin ƙara wayar da kai kan sabbin dokokin gyaran haraji da kuma ƙarfafa bin doka a fadin jihar.
Ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan sabbin gyare-gyaren tsarin haraji na jihar, manufofin daidaita biyan haraji, da kuma sabuwar manhajar haraji ta zamani (E-taɗ portal) da aka ƙaddamar.
A cewarsa, “shirin an tsara shi ne don wayar da kan masu ruwa da tsaki kan sabbin ci gaban da aka samu a tsarin haraji na jihar, tare da fayyace rawar da kowane ɓangare ke takawa ƙarƙashin sabbin dokokin.
“Wannan shiri, wanda PACE ke tallafawa gaba ɗaya, yana da nufin ilmantar da masu ruwa da tsaki game da sauye-sauyen da ke gudana a hukumar tara haraji ta jihar da kuma muhimman sashe-sashen dokokin haraji na ƙasa.
“Manufar ita ce tabbatar da bin doka, ƙarfafa gaskiya da bayyana gaskiya a harkokin haraji, da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga domin gwamnati ta inganta ayyukan da ke amfani ga jama’a,” inji shi.
Abubakar ya jaddada muhimmancin samun Lambar Haraji (TIN) ga duk masu biyan haraji, yana mai cewa hakan wajibi ne bisa tanadin sashe na 8 na Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya.
Ya ce duk wanda yake da hurumin biyan haraji dole ne ya mallaki TIN, wanda ake yin ta kyauta ta yanar gizo ko a ofishin KIRS mafi kusa.
