Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna
Shugaban ƙungiyar Northern Stakeholders Initiatiɓe, Yerima Usman Shettima, ya roƙi ‘yan Nijeriya da su riƙe fata nagari da haɗin kai yayin da ƙasar ke bikin cikar shekaru 65 da samun ‘yancin kai.
Yayin da yake jawabi a wani biki da aka gudanar a Kaduna wanda ƙungiyar mahaya manyan babura (power bike) URMC Bikers tare da haɗin gwiwar Capacity Moɓement suka shirya, Shettima ya ce tsayuwar Nijeriya duk da ƙalubale da dama da ta fuskanta alama ce ta cewa har yanzu ƙasar tana da makoma mai kyau.
Ya ce, “Abin da ya sa muka kasance ƙasa ɗaya har yanzu abin murna ne. Ko a cikin lokaci mai tsauri, ina ganin haske, haka ma ‘yan Nijeriya su na ganin sa. Ko da ya ya wuya, akwai fata a ƙarshe,” inji shi.
Shettima ya nuna cewa matsalar tsaro da kuma wahalhalun tattalin arziki sun yi tasiri a kan ‘yan ƙasa, amma ya dage da cewa daidaito ya fara dawowa a hankali.
Ya ƙara da cewa bukukuwan ranar ‘yancin kai bai kamata kawai su kasance na tunawa da sadaukarwar shugabannin ƙasa na farko ba, har ma ya zama kira na zaman lafiya, juriyar zuciya da kuma imani da ƙasa.
“Shekaru sittin da biyar ba ƙaramin tafiya ba ne. Amurka ta yi fiye da shekaru 200 ta na murna, mu ma za mu kai can. ‘Yan Nijeriya dole su kasance masu zaman lafiya su kuma mara wa gwamnati baya don ta iya isar da ayyukan ta,” inji shi.
Sai dai ya jaddada cewa haɗin kai da haƙuri su ne ginshiƙan da za su tsare ƙasar.
A kan kiraye-kirayen da Capacity Moɓement ke yi masa da ya tsaya takarar kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a 2027, Shettima ya ce ana ci gaba da tattaunawa.
Ya ce, “Na ji kiran su. Nan da wani lokaci zan ba da amsa yadda ya kamata. Da fatan, ‘yan Nijeriya za su san matsayi na a lokacin da ya dace.”
Shi kuwa shugaban Capacity Moɓement na ƙasa, Shehu Sani Sado, ya ce ƙungiyar na goyon bayan Shettima ne saboda yana ɗauke da halayen da ake buƙata wajen samar da jagoranci na gari.
ƙungiyar mahaya baburan da ƙungiyar Capacity Moɓement sun shirya bikin ne don taya ‘yan Nijeriya murnar cika 65 da samun ‘yancin kai, wanda aka gudanar a filin wasa na Centenary Park da ke kusa da gidan gwamnatin Jihar Kaduna.
Yerima Shettima ya kasance ɗaya daga cikin ‘yan ƙungiyar URMC, sannan ƙungiyar Capacity Moɓement kuma, ita ce ƙungiyar da ta ke ta fafutukar neman sa da ya tsaya takarar sanata a Kaduna ta Tsakiya.
Haƙiƙa an baza capacity a titunan Jihar Kaduna. Domin kuwa Yerima jagoranci hawa mahayan.
Bayan dawowa daga zagaye, an gudanar wasan motoci da babura (stuns).
Haka kuma an yi gagarumin biki (Haka Night) domin karrama baƙin da suka zo daga wasu garuruwan. An yi bikin ne a ɗakin taro na Command Guest House, Kaduna.
