Rashin bai wa mata dama na daƙile cigaban Nijeriya – Sarki Sanusi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a ranar Alhamis ya yi kira da a gudanar da sauye-sauye na musamman domin rushe shingayen da ke hana mata a Nijeriya cikakken shiga harkokin siyasa, kasuwanci da shugabanci.

Da yake jawabi a taron Gender Impact Inɓestment Summit na uku a da ya gudana a birnin Legas, Sanusi ya bayyana cewa samar da daidaito tsakanin maza da mata ba sadaka ba ce, illa dai wani lamari ne na hankali da adalci. Ya buƙaci a yi gyaran kundin tsarin mulki da kuma tsarin ɓangaren kuɗi don tabbatar da karin wakilci ga mata.

“Muna da Sanatoci 109 amma mata huɗu ne kacal. Ta yaya za a samar da dokoki da ke kare mata alhali kuwa ba a jin muryoyinsu sosai?” in ji shi.

Ya bayar da shawarar a ware kowace jiha ta samu akalla kujerar Sanata mace a tsarin, tare da sanya kaso na musamman na mata a cikin ministoci.

Sarki Sanusi wanda ya jagoranci Babban Bankin Nijeriya daga shekarar 2009 zuwa 2014, ya tuna cewa kafin shugabancinsa na babban banki mata huɗu ne kawai suka kai matsayi na darakta. Ya ce sauye-sauyen da ya kawo lokacin mulkinsa sun taimaka wajen ƙara adadin mata a manyan mukamai, inda suka fara jagorantar muhimman sassa kamar kula da bankuna da kuma kula da jagoranci.

Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauyen sun shafi dukkanin harkar banki a ƙasar nan, lamarin da ya kai ga ƙaddamar da shirin “Shekarar Mata a tsarin Banki” a shekarar 2012, wanda daga bisani bankuna tara suka samu shugabanni mata a matsayin Daraktocin gudanarwa.

Sarkin na Kano ya kuma bukaci hukumomin kula da hannayen jari (SEC) da Hukumar Inshora ta Kasa (NAICOM) da su tilasta cibiyoyin kuɗi su rika wallafa rahotanni bisa bambancin jinsi, musamman a harkar bayar da rance da ɗaukar ma’aikata. Ya ce wannan bayyananniyar hanya za ta ƙara adalci da kulawa wajen tallafa wa kasuwancin da mata ke jagoranta.

Kazalika, ya jaddada cewa dole a magance shingayen al’adu, inda ya yi nuni da cewa a harkar noma mata kan rasa riba duk da cewa su kan gaji gonaki.

“Mafita dole ta dace da yanayin al’adu da zamantakewar kowace al’umma. Abin da ya dace a Maiduguri watakila ba zai dace a Warri ba,” in ji shi.

Shi ma a nasa jawabin Ministan Harkokin Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Geoffrey, ya tabbatar da cewa gwamnati na da kudurin ganin mata ba a ware su wajen tsara makomar tattalin arzikin Nijeriya.

A nasa ɓangaren, shugaban Impact Inɓestors Foundation, Frank Aigbogun, ya yaba da sabuwar taswirar shekaru goma da aka kaddamar, wacce ta kuduri aniyar tara dala biliyan takwas ($8bn) domin zuba jari a harkokin da suka shafi mata, matasa da kuma masu bukata ta musamman, don cike gibin rashin samun kuɗaɗe da kuma ci gaba.

By ukarofi