Fitaccen ɗan dambe ɗan asalin Nijeriya, Anthony Joshua, na iya komawa ƙasar mahaifansa domin yin gagarumin fafatawa da abokin hamayyarsa Martin Bakole a wani babban gasa da ake shirin kira “Rumble in the Jungle II”, wanda ake sa ran gudanarwa a birnin Legas cikin shekarar 2026.
Rahotanni daga majiyoyi kusa da masu shirya gasar sun bayyana cewa an kammala tattaunawa tsakanin Joshua da hukumar wasanni ta Nijeriya (NSC), tare da tallafin wasu manyan kamfanonin sadarwa da bankuna da ke son ɗaukar nauyin taron. Idan wannan lamari ya tabbata, zai zama karo na farko da Joshua zai yi fafatawa a wasar da mahaifansa suka fito — bayan shekaru da dama yana yin dambensa a Birtaniya da Amurka.
A cewar manajan sa, Eddie Hearn, Joshua yana ganin wannan dama a matsayin “komawa gida domin cika alƙawarin da ya daɗe yana yiwa masoyansa.” Ya ce: “Anthony na da burin kawo babban gasa a Nijeriya, domin ya nuna cewa ƙasashen Afirka ma za su iya karɓar manyan wasannin duniya cikin kwarewa.”
Wannan fafatawa za ta tuna wa mutane da tarihi, domin taken “Rumble in the Jungle II” yana nuni da sanannen fafatawar da Muhammad Ali ya yi da George Foreman a Zaire ( yanzu Congo) a 1974 — wanda ya zama ɗaya daga cikin manyan tarukan dambe da aka taba gudanarwa a Afirka.
Bakole, wanda ke da asalin Congo amma yana wakiltar Scotland, ya ce shi ma yana son wannan fafatawa ta zama tarihi. “Ina son in buga da Joshua a ƙasa mai cike da tarihi. Wannan ba kawai wasa ba ne, gasa ce tsakanin ‘ya’yan Afirka biyu,” inji shi.
Masana wasanni a Nijeriya sun fara bayyana wannan shiri a matsayin damar da za ta sake jawo hankalin duniya kan ƙasar, musamman wajen farfaɗo da harkar dambe da ta taɓa yin fice a shekarun baya. Wasu kuma na ganin hakan zai buɗe ƙofofin zuba jari a fannin wasanni da yawon shakatawa.
Joshua, wanda ke da rikodin nasarori 27 cikin fafatawa 30, ya bayyana cewa yana cikin shiri na musamman tare da sabbin masu horarwa a Amurka. Ya ce manufarsa ita ce “ta dawo da kambunsa da kuma kawo farin ciki ga ‘yan Nijeriya.”
Idan gasar ta tabbata, za a gudanar da ita a filin wasan Teslim Balogun Stadium ko kuma sabon Eko Arena da ke cikin tafkin Legas — kuma za a yada ta kai tsaye a kafafen duniya kamar DAZN da Sky Sports.
