
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Lahadi Shugaba Bola Tinubu zai je Rome, Babban Birnin ƙasar Italiya daga Abuja domin halartar zaman shugabannin ƙasashe na ‘Aqaba Process’, wanda zai mayar da hankali akan matsalolin tsaro da suka shafi yankin Yammacin Afirka.
Za a fara zaman ne a ranar 14 ga watan nan na Oktoba, inda jagororin ƙasashe da manyan jami’an tsaro na gwamnatoci za su haɗu da wakilan ƙungiyoyin gwamnati da waɗanda ba su ba domin tattauna batutuwan ƙalubalen tsaro a shiyyar.
A shekarar 2015 Sarki Abdullah na II na ƙasar Jordan ya samar da tsarin zaman shugabanni da ya yi wa laƙabi da ‘Aƙaba Process’ da nufin tattauna hanyoyin magance matsalolin rashin tsaro.
Zaman ya kuma ƙunshi tattaunawa akan yadda ayyukan ƴan ta’adda ke cigaba da faɗaɗa a Afirka ta Yamma musamman a yankunan sahara da ruwa.
Daga cikin waɗanda za su yi wa shugaban ƙasar rakiya akwai Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegu Ojukwu; Ministan Tsaro, Badaru Abubakar; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA) Nuhu Ribaɗu; Darakta-Janar na Hukumar Leƙen Asiri (NIA), Mohammed Mohammed da wasu manyan jami’an gwamnati, kamar yadda kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana a wata takarda.
