Rashin lafiya: Gwamnan CBN zai maye gurbin Ministan Kuɗi a zaman IMF

Spread the love

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso zai jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron shekara-shekara na Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Ƙasa-da-Ƙasa (IMF) da za a gudanar a birnin Washington DC daga ranar Litinin, 13 ga Oktoba.

Olayemi Cardoso zai wakilci Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙin Ƙasa, Mista Wale Edun, wanda ba zai samu damar halarta ba sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sannan daga cikin tawagar Nijeriyar akwai Ƙaramar Ministar Kuɗi, wato Doris Uzoka-Anite da wasu manyan jami’an gwamnati.

A cewar Bankin Duniya, muhimman abubuwan da za su gudana a taron sun haɗa da Zaman Babban Kwamitin Ci-Gaban Duniya (Development Committee Plenary) a ranar 16 ga Oktoba, da kuma Zaman Kwamitin Kuɗi na Ƙasa-da-Ƙasa (International Monetary and Financial Committee) a ranar 17 ga Oktoba.

Haka kuma, za a gudanar da tattaunawa na yankuna, tarukan manema labarai, da muhawarori kan ci-gaban duniya, tattalin arziƙin ƙasashe da kasuwannin kuɗi.

Wannan rahoton ya fito ne daga ofishin Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga a ranar 12 ga Oktoba, 2025.

By Babaji