Sufeto Janar ya sauya wa kwamishinan Abuja wajen aiki kan kisan ƴar jaridar Arise News

Spread the love

Sufeto Janar na Ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ƴan sandan Birnin Tarayya Abuja, Ajao Adewale daga muƙaminsa.

Kodayake ba a bayyana dalilin sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa an yi hukuncin ne duba da yadda rundunar ta Abuja ta gudanar da batun gilashin mota mai duhu da kuma kisan ƴar jaridar Arise News, Sommie Maduagwu a ƴan kwanakin nan.

Ana ganin waɗannan matsaloli biyu ne suka haifar da sauya masa wajen aikin zuwa wajen da ya fi dacewa da ƙwarewarsa.

Wata majiya ta ce, Sufeton Janar ɗin ne zai bayyana hakan wajen za a mayar da shi a nan gaba, tare da jaddada cewa Adewale ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a matsayin kwamishina.

Kakakin rundunar ƴan sanda ta ƙasa, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da wannan sauyi, inda ya bayyana shi a matsayin al’ada da ake aiwatarwa lokaci zuwa lokaci domin inganta ayyukan jami’ai a hukumar.

By Babaji