
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya miƙa saƙon taya murna ga ɗansa Seyi Tinubu, wanda ke cika shekaru 40 a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin kamili mai mayar da hankali akan al’amuransa masu amfani, lamarin da ke tasiri acikin al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.
A wata takarda da Tinubu ya fitar a jiya Lahadi, Shugaban ƙasar ya yaba wa ɗan nasa akan yadda yake da ƙwarewar shugabanci da ƙoƙarin gina al’umma yana mai bayyana hakan a matsayin abin alfahari ga Nijeriya.
Ya ce, Seyi ya kasance mai jajircewa akan ababe masu amfani tun a ƙurciyarsa musamman wajen tunkarar ƙalubale, wanda hakan ya sa yake samun nasarori a kasuwancinsa da hidimar al’umma.
Ya ƙara da cewa, wannan mataki da Seyi ya kai na shekara 40 abin godiya ne bisa la’akari da tsayuwa akan horon da ya dace da rayuwa da jajircewa, wanda ya zama ƙashin baya ga ahalinsu.
Haka kuma, Tinubu ya yabi sadaukarwar Seyi ga gidansa duba da yadda yake kula da iyalansu.
A ƙarshe, ya masa addu’ar fatan samun albarkar Allah a dukkanin al’amuransa da samun shekaru masu albarka a gaba.
