Magoya bayan Kano Pillars sun farmaki ƴan wasa bayan Shooting Stars ta farke ana dab da tashi

Spread the love

An samu tashin hankali a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar Kano a yayin wasan da ya gudana tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars da Shooting Stars (3SC), bayan da magoya bayan Kano Pillars suka mamaye filin wasa cikin fushi sakamakon farke kwallon da baƙuwar ƙungiyar ta yi.

Rahotanni sun bayyana cewa magoya bayan sun kai hari kan alƙalin wasa, wanda ya tsere domin tsira da ransa, yayin da wasu daga cikin ƴan wasan 3SC suka gamu da farmaki.

Daga bisani, jami’an ‘yan sanda da ke tsaron filin sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa masu tayar da hankalin da kuma dawo da zaman lafiya a filin wasan.

Zuwa yanzu Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasa (NFF) ba ta fitar da sanarwa akan lamarin ba, yayin da ake jiran cikakken rahoto daga jami’an tsaro da hukumomin da al’amarin ya shafa.

By Babaji