Ba aiki ba albashi – Gwamnatin Tarayya ga ASUU

Spread the love

‎Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da cewa duk wani malami da ya shiga yajin aikin gargaɗi da ƙungiyar ta sanar, ba za a biya shi albashi ba a lokacin.

A wata takardar haɗaka tsakanin Ministan Ilimi Tunji Alausa da Ƙaramar Ministar Ilimi, Suwaiba Sa’id suka fitar, Ma’aikatar ta bayyana cewa gwamnati ba za ta amince da biyan albashi ga malaman da ba su je aiki ba domin ba a biyan albashi ga wanda bai yi aiki ba.
‎
‎Gwamnatin ta jaddada cewa ƙofa a buɗe take don cigaba da tattaunawa da ƙungiyar, amma hakan ba zai hana ta aiwatar da dokar ‘no work, no pay’ ba, wato ‘ba aiki, ba albashi’.
‎
‎Gargaɗi na zuwa ne jim-kaɗan da ASUU ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin gargaɗi na mako biyu sakamakon zargin gwamnati da gaza cika alƙawuran da ta ɗauka tun a shekarar 2009.
‎
‎Ƙungiyar ASUU ta ce, ta ɗauki wannan mataki ne domin tilasta gwamnati ta kula da halin da jami’o’in ƙasar ke ciki, musamman batun albashi, kayan aiki da kuma ingancin karatu.
‎
‎Duk da haka, gwamnatin ta ce za ta cigaba da gudanar da harkokin jami’o’i tare da kare muradun ɗalibai da ƙasa baki ɗaya.

By Babaji