Likitoci a Asibitin Deɓnandani da ke yankin Hapur a ƙasar Indiya, sun yi nasarar cire wasu baƙin ababe a cikin wani mara lafiya mai kimanin shekaru 40 bayan masa wani aiki na tsawon sa’o’i biyar a farkon wannan watan.
A ranar 17 ga watan Satumbar da ta gabata aka kwantar da shi sakamakon ciwon ciki mai tsanani, amai da kasala.
A yayin da ake masa aikin ne aka yi arangama da cokulan silba guda 29, alburushi 19 da biro biyu.
Aikin haska ciki da aka yi gabanin haka ya nuna wani baƙon yanayi, lamarin da ya girgiza tawagar likitocin.
Babban likitan da ya jagoranci aikin, Dakta Shyam Kumar ya ce, “ban taɓa baƙin abubuwa da dama haka acikin mara lafiya ɗaya ba.” Ya bayyana cewa, sai da suka farfasa su kafin suka fitar da su.
Jami’an asibiti sun ce da fari an garzaya da mara lafiyan zuwa wata cibiyar kula da marasa lafiya na musamman na ƙwaƙwalwa a Ghaziabad, inda a nan ya fara haɗiye ababen don nuna fushi akan kai shi wajen.
ƙwararrun akan harkar lafiya sun ce hakan da ya yi ka iya yiwuwa saboda taɓin hankali ne da ya same shi, wanda ke kai wasu cin ababen da ba a ci.
