DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Tarayya ta umarci a dakatar da biyan albashin ‘yan ASUU

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da biyan albashin malaman jami’o’in da suke ƙarƙashin ƙungiyar ASUU da ta shiga yajin aiki a yau Litinin.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ya sanar da umarnin hakan a cikin wata takarda da ya sanya wa hannu, inda ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da biyan albashi ga ma’aikatan da suka daina aiki ba, bisa ka’idar “no work, no pay.”

A cewar ministan, Gwamnatin Tarayya tana buɗe ƙofa ga tattaunawa da ƙungiyar ASUU domin magance matsalolin da suka jawo yajin aikin, amma ta jaddada cewa za a cigaba da aiwatar da dokokin gwamnati har sai an samu maslaha a tsakanin ɓangarorin.

Wannan mataki na zuwa ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu mambobin ASUU a wasu jami’o’in tarayya sun dakatar da koyarwa saboda rashin aiwatar da wasu yarjejeniyoyi da aka cimma a baya tsakaninsu da gwamnati.

By Babaji