By SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗaruruwan ma’aikatan da gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da abashin su kimanin watanni Takwas da suka gabata, sun gudanar da addu’a ta musamman don neman agajin gaggawa gurin Allah.
Shamsuddeen Muhammad Soja, wanda mataimakin shugaban ƙungiyar ma’aikatan da gwamnatin ta dakatar, a zantawar sa da wakilin mu, ya bayyana cewar, su kimanin 3000 ne matsalar ta shafa .
A cewar sa, sunyi duk ƙoƙarin da ya dace Wajen tuntuɓar gwamnatin jihar don kawo ƙarshen matsalar su amma abun ya gagara.
Soja ya ƙara da cewar, a ƙarshe sunje ofishin shugaban ma’aikatan jihar, inda ya tabbatar masu cewar babu wani abun da zai yi a kai.
“Mun samu mai girma Gwamna Dauda Lawal, lokaci da dama, yayi mana rantsuwa da Allah cewar za a dawo damu bakin Aikin mu amma hakan bata samu ba, hakazalika daga ƙarshe shugaban ma’aikatan jihar ya tabbatar mana cewar an kore mu”. Shamsuddeen yace
Hakazalika, ya ƙara da cewar sun shirya gangamin addu’ar ne domin su nemi agaji gurin Allah, yana mai nuni da cewar addu’ar an gudanar da ita a kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 14 dake jihar.
“Mu tsara yin wannan addu’a a kowace ƙaramar hukuma kuma zamu cigaba da yin ta don neman agajin gaggawa gurin Allah madaukakin Sarki dangane da matsalar mu”.
Shamsuddeen Muhammad yayi Kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da ta dubi galin da suke ciki, ta dawo dasu aikin su don rayuwar su ta samu sauki.
“Mutanen mu na cikin mawuyacin hali, yawancin mu munada iyali, Muna kira ga gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Dauda Lawal da ta dubi halin da mu ke ciki ta dawo damu bakin aikin mu don rayuwar mu ta cigaba”.
Idan za a iya tunawa, a watan Fabrairun wannan shekara ne gwamnatin Jihar Zamfara ta ayyana cewar, ta bankaɗo ma’aikatan bogi su 2363 a yayin aikin tantance ma’aikatan Jihar don aiwatar da mafi ƙarancin abashin 70,000.
A wata mai kama da wannan, jam’iyyar APC a jihar tayi Allah wadai game da matakin da gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauka na korar ma’aikatan su fiye da 3000.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ta APC a jihar, Yusuf Idris ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau a Gusau.
Sanarwar ta bayyana cewar mafiya yawan waɗanda aka kora suna daga cikin ma’aikatan da gwamnatin da ta gabata ta Dr. Bello Mohammed Matawalle ta ɗauka, yana mai nuni da cewar matakin da gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauka wani salon rashin tausayawa alummar jihar ne.
“Sanin kowa ne gwamnatin Dr. Bello Mohammed Matawalle kuma ƙaramin ministan tsaron Nigeria ta ɗauki sama da matasa 1,400 aiki, ƙari da malamai 336 da kuma ma’aikatan lafiya 200. Amma wannan gwamnatin duk ta dakatar da su aiki”. Cewar Yusuf
“Saboda haka jam’iyyar APC a Jihar Zamfara tayi Allah Wadai da wannan mataki, domin waɗanda abun ya shafa, yan Jihar Zamfara ne, kuma suna da iyali, amma gashi an jefa su cikin mawuyacin hali har wasusn su sun fara barace barace”. A cewar Yusuf
Jam’iyyar ta APC tayi Kira ga gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal da ta gaggauta dawo da ma’aikatan aikin su don rayuwar su ta samu inganta.
