
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Fafutukar Walwalar Al’umma a Nijeriya (MEN) ta koka game da yadda har yanzu ake cigaba da tsare sanannen mataimakin kwamishinan ƴan sandan nan, DCP Abba Kyari duk da cewa a kwanan nan ƴan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, ƴan damfara da masu garkuwa da mutane da aka kama (waɗanda da dama tawagar jami’in ne ta kama su) ko yanke wa hukunci, suka samu shiga sahun waɗanda aka yi wa yafiyar shugaban ƙasa.
MEN, a wata takarda da Kwamared Janar ɗinta, kuma tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung ya fitar, ta ce zaɓen wasu da nufin yi musu afuwa da kuma ware wasu rashin adalci ne da ƙoƙarin haifar da koma-baya ga jagoranci mai ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci.
Ta ce, idan har sanannun ƴan ta’adda sun cancanci a yi musu afuwa a Nijeriya, to cigaba da tsare jami’in tsaro da aikinsa shi ne ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci ba daidai ba ne, hasali ma shi ne ya fi dacewa a yi wa afuwa.
Ƙungiyar ta bayyana hakan a matsayin butulci ga mutumin da ya sadaukar da kansa tare da jefa rayuwarsa cikin haɗari domin tsaron ƙasa da tabbatar da doka da oda acikin al’umma.
Kazalika, ta ce hakan wani nau’i ne rashin tausayi a harkar shari’a ganin yadda ake iya yafe wa masu laifi yayin da ake cigaba da hukunta na gari.
Akan haka ne ta kiyayi Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu da Antoni-Janar da su dakatar da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi wa DCP Abba Kyari tare da umartar gaggauta sako shi.
