Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa shekaru goma na shugabancin Farfesa Mahmood Yakubu (2015–2025) sun zama wani lokaci na sauye-sauye masu zurfi a tarihin gudanar da zaɓe a Nijeriya.
A cikin rahotanni biyu da ta fitar — Election Management in Nigeria: 2015–2025 da Innovations in Electoral Technology: 2015–2025 — hukumar ta ce wannan lokaci ya inganta amfani da fasahar zamani, ya ƙarfafa doka, ya faɗaɗa damar masu zaɓe, tare da aara gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.
Yakubu, wanda aka naɗa a 2015 daga tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, sannan aka sake naɗa shi a 2020, shi ne shugaban farko na INEC da ya kammala wa’adin shekaru goma gaba ɗaya. Lokacinsa ya haɗa da manyan zaɓe biyu — na 2019 da 2023 — da kuma zaɓen gwamna a jihohi 19 da ƙarin ɗaruruwan zaɓe na cike gurbi a faɗin ƙasa.
A ƙarƙashinsa, INEC ta ƙaddamar da muhimman sauye-sauye kamar tsarin Bimodal Voter Accreditation System (BVAS), INEC Result Viewing Portal (IReV), da INEC Voter Enrolment Device (IVED) — waɗanda suka juyar da tsarin gudanar da zaɓe daga tsohon salo zuwa tsarin fasahar zamani mai inganci.
Yakubu ya amince a cikin gabatarwarsa cewa hukumar ta fuskanci aalubale irin su cin hanci da rashawa, tashin hankali, da tsangwama ta kotuna. Sai dai, ya ce hukumar ta ɗauki matakan gyara da haɗin gwiwa da jami’an tsaro domin kare amincin tsarin.
Rahoton ya bayyana cewa tun 2021, hukumar ta fara amfani da na’urar IVED wajen rijistar masu zaɓe ta hanyar ɗaukar hoton fuska da yatsun hannu, sannan ta ƙaddamar da shafin CVR Online Portal domin ba ’yan ƙasa damar yin rajista daga gida — karo na farko a tarihin ƙasar.
Haka kuma, an bayyana cewa BVAS da IReV, waɗanda dokar zaɓe ta 2022 ta ƙarfafa, sun zama ginshiƙan tabbatar da ingantattun zaɓe a Nijeriya.
INEC ta ce, “fasaha ta zama ginshiƙi na ɓoye amma mai ƙima wajen tabbatar da sahihancin zaɓe, tun daga tantancewa har zuwa watsa sakamakon zaɓe kai tsaye ga jama’a.”
