Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa kafin ƙarshen wa’adin farko na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a 2027, babu wani alƙalin Abuja da zai ci gaba da zama a gidan haya.
Wike ya bayyana haka ne a Abuja ranar Litinin, yayin ƙaddamar da aikin gina sabbin gidaje na musamman ga manyan shari’a — ciki har da shugaban Kotun ɗaukaka ƙara, Alƙalin Alƙalai na Babban Kotun Tarayya, na Babban Kotun Abuja, da shugaban Kotun ƙwadago.
Ya ce, wannan shiri na daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na inganta walwalar ma’aikatan shari’a da ƙarfafa musu gwiwa wajen gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali.
“Na gaya wa shugaban ƙasa cewa dole mu bambanta salonmu wajen kula da walwalar alƙalanmu. Ba za mu ci gaba da ganin su na zama a gidajen haya ba. Wani lokaci ba su san masu gidajen ba, ko maƙwabta ba — alhali su ne ke yanke hukunci kan manyan laifuka,” inji Wike.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin Tinubu ta ɗauki alƙawarin tabbatar da cewa alƙalan ƙasar za su samu muhallin da ya dace da matsayinsu kafin ƙarshen wa’adin mulkinsa.
Wike ya tabbatar wa shugabannin kotuna cewa aikin gine-ginen zai kammala cikin watanni 12, kuma takardun mallakar gidajen za su kasance a sunayensu domin su zama nasu bayan ritaya.
Ya bayyana cewa aikin gine-gine na gidaje 40 da ke gudana — gidaje 10 na alkalan kotun ɗaukaka ƙara, 10 na Babban Kotun Tarayya, da 20 na Babban Kotun FCT — za a kammala su kafin ƙarshen wannan shekara.
Haka kuma, Wike ya tabbatar wa shugaban Kotun ƙwadago ta ƙasa, Mai Shari’a Benedict Kanyip, cewa alkalan kotun ma za su amfana da irin wannan shiri.
A nata jawabin, Ministan Jiha ta FCT, Dokta Mariya Mahmoud, ta ce aikin na nuni da himmar gwamnati wajen ƙarfafa ginshiƙan adalci da mulki nagari a babban birnin ƙasa.
“Wannan aiki alama ce ta mutunci da girmamawa — na samar da gidaje masu dacewa da matsayi ga shugabannin kotunanmu waɗanda hikima da gaskiyarsu ke riƙe da dokokin ƙasa,” inji ta.
A nasa ɓangaren, Mai Shari’a Kanyip ya gode wa Tinubu bisa amincewa da aikin, yana mai cewa samar da gidaje masu tsaro da kwanciyar hankali zai taimaka wajen tabbatar da cikakken ‘yancin shari’a.
“Alƙalanmu za su yi aiki cikin kwanciyar hankali idan aka tabbatar musu da tsaro da walwala. Wannan shirin gidaje zai taimaka wajen kawar da damuwa, domin su mai da hankali kacokan kan aikinsu,” inji shi.
Ya kuma tunatar da cewa samar da gidaje ga alƙalan ƙasa na cikin haƙƙoƙin da kundin tsarin mulki na 1999 ya tanada.
