Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Bauchi kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP a ƙasa, Sanata Bala Mohammed, ya ce jam’iyyar za ta maye gurbin gwamnoninta da sauran ‘yan siyasar da suka fice zuwa jam’iyyar APC da mutane masu ƙarfi, amana, da nagarta kafin zaɓen 2027.
Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Abuja yayin da yake tattaunawa da manema labarai game da shirin taron gangamin zaɓen shugabannin jam’iyyar da za a gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga Nuwamba.
Ya amince cewa ficewar wasu gwamnonin PDP zuwa APC abin damuwa ne, amma ya tabbatar cewa jam’iyyar za ta fito daga wannan yanayi da ƙarfi.
“Idan ka tambaye ni ko ina cikin damuwa da ficewar gwamnoninmu, eh, ina cikin damuwa sosai. Amma shugabanci nauyi ne,” inji shi. “Kowa yana da ‘yancin yanke shawara, amma muna aiki a bayan fage domin gyara komai.”
Wannan jawabi nasa ya zo ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Gwamna Peter Mbah na Enugu zai koma APC, bayan irin wannan mataki daga gwamnonin Akwa Ibom da Delta a baya-bayan nan.
Gwamnan ya zargi gwamnatin tarayya mai mulkin APC da amfani da ƙarfin mulki wajen raunana adawa, yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin tsarin jam’iyya ɗaya.
“Salon mulkin APC shi ne su maida ƙasar jam’iyya ɗaya. Suna da ƙarfin tilastawa, suna da duk wata hanya,” inji Mohammed.
Ya ce duk da cewa kowa na da ‘yancin yanke shawara, “mutanen ƙasa ba su farin ciki da masu ficewa saboda mafi yawansu ‘yan PDP ne.”
Mohammed ya nuna ƙwarin gwiwar cewa PDP ita ce jam’iyyar da ‘yan Nijeriya har yanzu ke amincewa da ita wajen samar da shugabanci na gaskiya.
“Akwai fice-fice saboda wasu lissafin siyasa ne kawai, amma ni ba na ko da niyyar barin PDP. Bauchi jam’iyyar PDP ce kuma za ta ci gaba da kasancewa haka.”
Ya ƙara da cewa, PDP ce kawai jam’iyyar adawa da ke da tsari mai ƙarfi da shugabanci mai ɗorewa a ƙasa tun 1999, tana riƙe da tambari, tuta, da manufofinta.
Dangane da Gwamna Siminalayi Fubara na Rinas, Mohammed ya tabbatar cewa “yana nan cikin PDP, kuma yana aiki tuƙuru wajen haɗa kan mutanensa.”
Haka kuma ya ce jam’iyyar a shirye take ta maraba da manyan ‘yan siyasa da tsofaffin shugabanni kamar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan idan suka yanke shawarar dawowa.
A ƙarshe, Bala Mohammed ya ce PDP za ta yi amfani da taron gangamin Ibadan domin ƙarfafa haɗin kai, zaɓar shugabanni nagari, da shirya jam’iyyar don samun nasara a zaɓen 2027.
“Idan wasu sun tafi, hakan yana buɗe ƙofa ga sabbin gwaraza. Waɗanda aka raina sun riga sun tabbatar da cancantarsu, kuma hakan zai sake faruwa a 2027.”
