Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Nijeriya ta ƙulla sabuwar yarjejeniya ta sayen makamai da gwamnatin Pakistan, bayan ta sake nazarin tsohon kwangilar da ta tsaya cak sakamakon matsalolin fasaha da siyasa — lamarin da ke nuna ƙudurin gwamnati wajen ƙarfafa ƙarfin tsaron ƙasa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa News Point Nigeria cewa sabuwar yarjejeniyar, wacce aka cimma tsakanin Hukumar Samar da Kayayyakin Tsaro ta Nijeriya (DIS) da Ma’aikatar Samar da Makamai ta Pakistan, ta maye gurbin tsohuwar kwangilar da aka dakatar a watan Agusta 2025.
A ƙarƙashin wannan sabuwar yarjejeniya, Pakistan za ta samar wa Nijeriya da jirage K-8 guda 30 masu aikin horarwa da kai farmaki, jiragen leƙen asiri na Shahpar-II guda 40, jirage marasa matuƙi MR-10 guda 200, da kuma motocin yaƙi waɗanda harsashi ba ya ratsa su ASV Mohafiz-IV guda 230, da jimillar darajarsu ta kai dala miliyan 230.
Daraktan Hukumar DIS, Janar Mirghani Idris, ya tabbatar da wannan ci gaba bayan ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa birnin Islamabad, inda aka kammala tattaunawar tare da sanya hannu kan yarjejeniyar a gaban Ministan Samar da Makamai na Pakistan, Muhammad Raza Hayat Harraj, da manyan jami’an tsaro na ƙasar.
Majiyar ta bayyana cewa Nijeriya ta tilasta yin sabuwar tattaunawa bayan ƙasar Chana ta ƙi sayar da manyan makamai kamar Hƙ-9 da Hƙ-16, bisa manufarta ta ain shiga cikin rikice-rikicen ƙasashe ko waɗanda ke ƙarƙashin takunkumi. Pakistan kuma ta fuskanci cikas wajen samun injina da na’urorin kewayawa na jiragen MiG-21, wanda hakan ya sa aka gyara tsarin yarjejeniyar.
A sabuwar tsari, za a kawo jirage da motocin yaƙi ta tashar jiragen ruwa ta Port Sudan, yayin da jirage marasa matuƙi za su iso Wadi Sayyidna Air Base a Nijeriya bisa jadawalin da aka amince da shi.
Sabuwar yarjejeniyar za ta taimaka wajen ƙarfafa leƙen asiri da sa ido musamman a yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, tare da tabbatar da tsare-tsare bisa ƙa’idojin duniya da ingantaccen tsarin aiki.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Wannan mataki babbar nasara ce wajen bai wa dakarunmu kayan zamani don kare ƙasa. Muna tabbatar da cewa duk tsarin zai gudana cikin gaskiya da amana, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da Pakistan a fannin ƙera makamai da fasahar tsaro.”
