
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yiltwatda Goshwe ya sanar da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai kai ziyara Birnin Jos a jihar Filato domin karɓar sanannun ƴan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa cikin jam’iyyar.
Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na APC a ɗakin taro na otal ɗin Crest, Farfesa Yiltwatda ya ce ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar ya kai ziyarar nan da makonni biyu.
Ya bayyana cewa, ziyarar Shettima na da nufin ƙarfafa tubalin jam’iyyar da harkokinnta a jihar da ma shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Shugaban APCn ya ƙara da cewa hakan wata nasara ce ga jam’iyyar da kuma zama fage na janyo ra’ayoyin manyan ƴan siyasa a Nijeriya.
Kazalika, ya ce Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai da wasu gwamnoni sun tabbatar da halartar su taron.
Haka kuma, ya ce za a ƙaddamar da shirin raba Naira miliyan 100 domin inganta ƙananan ƴan kasuwa da nufin tallafa musu da sana’o’insu.
