Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamatin neman Jihar Karaɗua daga cikin Jihar Katsina, Alhaji Kabir Aliyu Maska , ya ƙaddamar da Kodinetoci 11 na ƙananan hukumomin shiyar domin faɗaɗa ayyukan su na neman Jihar Karaduwa.
A jawabinsa lokacin da yake ƙaddamar da ko’odinetocin, shugaban babban kwamitin zartarwar Alhaji Kabir Aliyu Maska ya bayyana cewa, a yayin taronsu na zartaswar an yanke shawarar a bai wa kodinetoci alhakin tafiyar da al’amuran ƙananan hukumomin su, dan samun gudunmuwa ta kowa da kowa dan ganin “haƙar mu ta cimma ruwa na neman Jihar Karaduwa,”Inji Maska .
Ya bayyana cewa duk da wasu matakai da tsare-tsare da suka wajaba idan aka bi su, akwai buƙatar masu gudanarwa su wayar da kan al’ummar karkara kan ƙoƙarin tabbatar da samun Jihar Karaduwa.
Kabir Aliyu Maska ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu kwamitin zartaswa ya gabatar da takarda ga kwamitocin Majalisar Dattawa da na wakilai kan samar da jihar Karaduwa a Kano da Kaduna a yayin taronsu na amsar buƙatun al’umma.
Shugaban ya ce an samu wani gagarumin ci gaba da kuma fatan alheri, domin sama da Sanatoci 72 ne suka amince da kudirin dokar sabuwar Jihar Karaduwa,wanda Sanata shiyar Funtúa Sanata Muntari Dandutse ya gabatar da ƙudirin a zauren majalisar”.
Kabir Aliyu Maska ya ci gaba da cewa yunƙurin samar da Jihar Karaduwa ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya”.
Ya bayyana jin daɗin sa ga maigirma gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa bisa goyon bayan da yake badawa ga yunƙurin samar da Jihar karaduwa.
Shima a nasa jawabin, Sakataren Ƙungiyar, Injiniya Tukur Lawal Funtua, ya buƙaci Kodinetocin su jajirce wajen ganin an cimma manufofin da ake buƙata na samun nasarar samun Jihar Karaduwa.
Ya bada tarihin yunƙurin samar da Jihar karaduwa wanda a cewar sa ya faro shekaru da dama da suka gabata.
Eng Tukur Lawal ya ce an tsara wani tsari na ganin cewa harkar ba ta taɓuka komai ba a wancan karon.
Sakataren ya kuma yi kira ga kodinetoci da ‘yan yankin na shiyyar Karaduwa da su ci gaba da jajircewa da bin doka da oda da Addu’a Koda yaushe dan samu nasara Jihar Karaduwa.
A nan take Sakataren Tukur Lawal ya bayyana Kodinetocin ƙananan hukumomin kamar haka , Hon Sagir Machika daga ƙaramar hukumar Sabuwa ,Ƙanƙara Hon Mashimu Jobe , Ɗandume Alhaji Musa Rabiu Mahuta ,Faskari Zubairu Muhammad Sheme, Funtua, Ibrahim Mu’azzam,Musawa Aminu Abdullahi San Inna,Matazu ,Isah Mazoji, Malumfashi Muktar.
Sai Ammani ,Danja Ibrahim SK,Bakori Hon Habibu Muhammad sai ƙaramar hukumar ƙafur Dr Bashir Yakubu Kagara.
Kodinetocin ta bakin wakilin su , Ibrahim SK na ƙaramar hukumar Danja ,ya bayyana cewa, lallai za su bazama wajen faɗakar da al’umma akan wannan gagarimin aiki da aka basu dan samun nasarar Jihar Karaduwa.
Daga cikin Kwamitin zartarwar na fafutukar neman Jihar Karaduwa da suka halarci taron sun haɗa ,Halilu Musa Ƙafur ,Hajiya Aisha Bakori,Iro Musa Anda Funtua da dai sauran su.
