Raddina ga Malam Lawan Triump

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Mudassir Bello Tudun Wada ya janyo hankali na zuwa ga wani Bidiyo da Mubarak Ibrahim Lawan ya saka a shafinsa mai mintuna 4 da dakikoki 2 inda Malam Lawan Triump ya bada bayanin raddi da Marigayi Sheikh Jafar ya min bayan na yi masa raddi akan taƙaddama a game da husufi na rana ko wata a shekarar 2006. Malam Lawan ya yi nasa raddin, yadda su ka saba yi, ba tare da kawo kwararan hujjoji ba sai babatu da kokarin cin fuska.

Zan yi kokari na kawo labarin tun asalinsa da irin hujjojin da na baiwa Marigayi Malam Jafar a wancan lokaci, hujjoji daga Qurani, kimiyya da hankali. Shi ma Malam Lawan zan kawo masa hujjoji wadanda mai karatu zai kalla ya yankewa kansa hukunci a kan matsalar gaba daya.

Idan mu ka yi waiwaye, a ranar Laraba, 29 ga watan Maris na shekarar 2006, rana ce wadda a ka dade ana dakonta sakamakon yayata zuwan husufin rana da kafafen yada labarai na duniya su ka yi makonni su na yi. Masana kimiyya sun yi hasashen cewa za’a sami husufi a wannan rana a fadin duniya wanda za’a ga cikakken husufin daga inda zai faro a kasar Brazil ya keto tekun Atalantika, ya bi ta arewacin Afirka ya ratsa tsakiyar Asiya inda zai kare daidai faduwar rana a yammacin Mongolia. Sauran kasashe da ba za su ga cikakken husufin ba, illa dai wani sashe nasa, sun hadar da kashi biyu cikin uku na kasashen Afirka har da Najeriya, da wasu kasashen Turai da tsakiyar Asiya. A wannan rana gidan rediyon Freedom ya gayyato Malam Jafar domin yi wa masu sauraro bayani a mahangarsa ta addini game da wannan husufi. Malamin ya yi kaca-kaca da masana kimiyya da nuna cewa abinda su ke fada duk karya ne domin ya sabawa Qurani da abinda manzon Allah ya fada. Jin haka, kasancewa kuma a lokacin ina da shiri da na ke gabatarwa duk mako a gidan rediyon na Freedom, inda na ke bayanin kimiyya da ayoyin Qur’ani a duk ranar Alhamis, don haka sai na shirya yiwa Malam Jafar Raddi.

Da farko dai na fara da kawo zargi da kalubalen da Sheikh Jafar ya ke wa masana kimiyya da cewa maganar da su ke yi na husufi na faruwa ne sakamakon wata na shiga tsakanin rana da duniya, ba daidai ba ne kuma ya sabawa ayar Qur’ani wadda ke cewa; Q36:40 “Rana ba ya kamata a gareta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukkansu a cikin wani sarari guda su ke yin iyo.”

A fassarar Malam Jafar wannan aya ta kore wancan ikirari na masana kimiyya da ke cewa wata ne ke shiga tsakanin rana da duniya idan an yi husufi, sannan kuma ya kara da wani hadisin da ke cewa idan ana husufi musulmi su shiga masallatai su yi ta addu’a domin zazzabi watan ya ke yi.

A cikin shiri na, na ambaci cewa dalilin da Sheikh Jafar da wasu malamai su ka yi wa wannan aya gurguwar fahimta shine, sakamakon ba su da ilimin kimiyya, domin da su na da ilimin kimiyya zasu gane cewa hakika wannan aya babu ta inda ta yi karo da bayanai na kimiyya game da lamarin husufi na Rana ko na Wata. Na ci gaba inda na bada sassaukan misali wanda ko wanda bai je makarantar boko da islamiyya ba, zai iya fahimtar hakan.

Na yi amfani da misali da agogon bango wanda ke da hannayen dakika, minti da awa wadanda ke cikin farantin agogon. Idan muka dauki farantin agogon inda wadannan hannaye ke zagaye a ciki, shine tamkar falaki (sararin samaniya) wanda Rana, Wata da Duniyarmu ke iyo a ciki, to hannayen dakika da na minti da na awa su ne a maimakon Rana, Wata da Duniyarmu.

Sai mu dauka cewa hannun dakika da ke sama shine rana, hannun minti da ke kasan sa kuma shine wata, sannan hannun awa wanda ke can kasansu kuma shine a matsayin duniya.

A misalin agogon, duk inda sha biyun rana ko na dare ya yi, wadannan hannaye duka na kasancewa a layi guda wanda ke tsaye a kan saitin sha biyu, to kamar haka ne duk sanda rana, wata da duniya a yayin kewayensu su ka jeru a saitin layi guda, shine sanda ake samun husufi, walau na rana ko na wata.

Idan husufin rana ne, sai mu dauka rana ce a matsayin hannun dakika, idan haskenta ya taho zai tarar da wata da ke tsakiya wanda zai hana hasken nan isa doron duniya da ke can kasa, maimakon haka sai inuwarsa ta fado kan doron duniya yadda wanda ke duniya idan ya kalli rana sai ya ga duhun wata da ya kare ta.

Haka abin yake a lokacin husufin wata inda duniya ke shiga tsakanin rana da wata yadda hasken rana wanda dama shi ke haskaka wata, sai duniya da ke tsakiya ta kare hasken yadda ba zai isa kan watan ba, a maimakon haka sai mu ga inuwar duniya ta rufe wata yadda zai zama baki babu haskensa.

Don haka duk da cewa wadannan halittu na Rana, Duniya da Wata, na iyo a sarari guda, babu wanda zai taba wani kamar yadda waccan aya ke cewa rana ba ta riskar wata, amma kuma idan su ka hau layi daya, wani na iya kare hasken wani isa wajen wani, abinda ke zama husufi ba tare da karya dokar wani ya tarar da wani ba. Wannan bayani na kimiyya ba inda ya yi karo da waccan aya ta cikin Yasin, sannan abu ne wanda a dubban shekaru aka tabbatar da shi.

Akasarin Malaman Musulmi a baya bayan nan, saboda koyarwa irin ta Izala, ya sa sun rufe kawunansu a akwati yadda ilimi ya wuce su, musamman na kimiyya. Wallahi ba za ka san girman Allah ba duk iliminka kamar yadda wanda ya san kimiyya. Kuma kimiyyar nan aikin Allah ce na yadda ya yi halittunsa, kuma asalinta malaman musulunci ne su ka assasa ta a duniya. Allah ya umarce mu da yin nazarin kimiyya cikin; Q45:3-5 “Lallai ne a cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga masu Imani, kuma a cikin halittarku da abinda ke watsuwa na dabba akwai ayoyi ga mutane masu Yakini. Kuma da sabawar dare da yini da abinda Allah ya saukar daga sama na arziki, sannan ya rayar da kasa game da shi a bayan mutuwarta, akwai ayoyi ga mutane masu yin hankali.”

Duk wani ilimi da ake neman Dan Adam yayi, ya fado a cikin wadannan ayoyi. Allah ya umarce mu da nazarin halittarmu (Biology) sammai (Astronomy) Kasa (Geography) dabbobi (Animals) Arziki daga sama (Climate and weather) Raya kasa bayan mutuwarta (Plants), kuma ta hanyar kimiyya ne zamu iya samun Yakini domin za ta bamu damar ganin abu a zahiri a aikace.

Malaman musulmin farko da su ka assasa kimiyya sun gamsu da yadda Annabi ya yaki camfi da azama musulmin farko wajen Nazari, musamman idan ka yi la’akari da hadisan cikin Bukhari, Muslim da kuma ruwayar Ibn Kathir cikin “Al-Bidaya Wa-l Nihaya” wanda ke cewa a ranar da dan Annabi, wato Ibrahim ya rasu, an yi husufin rana sai wasu sahabbai su ke cewa Allah ne ke yiwa manzonsa ta’aziyya. Nan take Annabi ya tara su ya ce “Husufin Rana ko wata, biyu ne cikin ayoyin ubangiji, ba sa faruwa domin mutuwa ko haihuwar wani”.

Annabi ya nuna mana karara cewa mu guji canfe-canfe mu yi nazarin ayoyin Allah ta hanyar kimiyya kamar yadda Allah ya umarta da kansa a Qurani, a matsayin hanya da zamu gane girman Allah da kudirarsa. Kuma babu wata hanya da ke iya nuna mana kudira ta zahiri irin kimiyya. 
Da ace Malam Jafar na nazarin kimiyya da zai gano cewa malaman musulunci ne su ka fara gano wancan tsari na yadda husufi ke wakana. Domin Al Khwarizmi (780-850 AD), mashahurin malamin lissafi kuma masanin ilimin sararin samaniya da duniya bata ga irinsa ba, shine ya kafa sassan lissafi na Algebra (wanda daga sunan littafinsa Al-Jabr ya samo asali) da sashen Algorithm (wanda daga sunansa Alkwarizmi, ake kiran sashen na lissafi kuma abinda ya kafa ginshikin da aka iya samun kwamfuta a yanzu).

Al-Khwarizmi ne malamin musulunci na farko da ya gano yadda husufi ke faruwa. Bayansa akwai: Al Kindi (801-873 AD), Ibn Yunus Al Misri (950-1009 AD), Al Haytham (965-1040 AD), Ibn Sina (980-1037 AD), Al Biruni (973-1048 AD) da Al Zarƙali (1029-1087 AD), duk wadannan malamai sun gano yadda husufi ke faruwa, su ka rubuta a littafansu, wanda daga wajensu turawa su ka dauka. Amma sakamakon malamai masu aƙida irin ta su Jafar, ba su yarda da sassan na ilimin kimiyya ba, face wani abu da yazo daga Salaf din da su ka Aminta da su.

Kuma wadancan Salaf din su ne su ka rayu da irin wadannan malamai, kuma su ka kafirta su, su ka hana a bibiyi nazarce nazarcensu, abinda su ka gadarwa na yanzu, yadda da ka saba da ra’ayinsu sai ayi waje-road da kai daga musulunci. Wannan dalili ya sa kimiyya, wadda musulmin farko su ka assasa, ta mutu murus a wajenmu domin ta zamanto abokiyar gabar Musulmi saboda muna zaton turawa ne su ka kawo ta.

Sakamakon amfani da ilimin kimiyya, mun kauce daga canfin cewa husufi na faruwa saboda mutuwa ko haihuwar wani, ko cewa wata ko rana na zazzabi ne. Shi ya sa a yanzu Dan Adam ke da ilimin gane cewa a nan gaba, yaushe irin wannan husufi zai sake wakana, a wace rana kuma a wane sashe na duniya, shin cikakken husufi za’a gani ko rabi? A yanzu haka, mai karatu ka rubuta ka ajiye ko na bar duniya, a ranar 14 ga watan Maris me zuwa na shekara 2025, inshallah, za a sami cikakken husufin wata, sannan a shekarar dai, wato ranar 7 ga watan Satumba na 2025 za a sake samun wani cikakken husufin na wata, haka kuma a shekarar 2027, ranar 6 ga watan Fabrairu za a samu cikakken husufi na rana. A takaice nan da shekaru 100 masu zuwa, za’a iya hasashen a wace rana za’a ga husufi na rana ko wata, domin tsari ne na lissafi da Allah ya kimsa cikin halittarsa yadda wata, duniya da rana kowanne na iyo a bigirensa kuma an san tsawon lokaci da nisan da kowanne ke dauka a zagayensa, tamkar yadda ka san cewa kwanaki 365 rana ke kewaye a shekara, ko kwanaki 29 da wata ke nasa kewayen.

Idan na koma kan Malam Lawan, kamar yadda a wannan bidiyo ya ce ya na wajen karatun Malam Jafar lokacin da ya yi raddi akan shirina na Freedom, to ban jin ya fadi gaskiyar abin yadda ni na sami labarin. Domin abu na farko dai na tabbatar bai ji shirina ba a wancan lokaci, domin da ya ji shirin ba zai ce hira aka yi da ni a Freedom ba, domin shiri ne na minti 30 a duk mako da na ke gabatarwa a kan kimiyya da Qur’ani mai suna “Tsokaci”. Sannan ko dai yayi wa Malam Jafar karya, inda ya ce a raddinsa na farko ya dauko ayar “Wa jumi’al shamsi wal ƙamar” ta cikin Suratul ƙiyama, domin ni a program dina babu inda na kafa hujja da ita domin bata da alaka kwata-kwata da yanayin Khusufi, kuma ko wanda bai san ilimin sararin samaniya ba, ba zai kawo ta ba ballantana ni da na dan san wani abu a kai.

Idan kuma ya tabbata Jafar din ita ya fara kawowa, to hakika Jafar din ya gaza a raddinsa domin baka wa mutum raddi sai akan abinda ya fada. Sannan ita kanta wannan ayar, wanda duk bai san kimiyya ba, sai dai kawai ya yi Imani da abinda Allah ya fada, amma ba zai fahimci ainihin yadda ayar ta ke ba. Domin su taurari kamar wannan rana ta mu, yadda ka ga mutane, haka Allah ya tsara su, wato ana haihuwarsu tun su na jarirai, sannan su girma, su balaga, su tsufa, daga karshe su mutu. Idan tauraro, kamar wannan Ranar ta mu ta zo mutuwa nan gaba, tare da tashin kiyamar duniya za su zo.

Domin a wannan lokaci za ta kumbura wanda wannan kumburi ko bai kone duniya ba, a yayin da ta yi bindiga, zata kone dukkan duniyoyi da ke kewayenta a kusa har da duniya. A wannan lokaci ka ga Allah ya hade rana da wata waje guda sun zama abu guda (Jumi’al shamsi wal ƙamar din ke nan). A wata ayar kuma ya kira abin da “Idan aka nike kasa, nikewa.’

Ni ayar da na kafawa Sheikh Jafar hujja da ita, ita ce dai waccan ta suratul Yasin da na kawo, wadda kuma da ita Jafar ya kafa hujja a shirinsa na Freedom wanda na ji da kunnena, kuma da ita na yi masa raddi na nuna cewa bai fahimce ta ba saboda karancin iliminsa na kimiyya. Kuma na kawo misali yadda ko wanda bai je makaranta ba zai iya ganewa ballantana wanda ya ke jin shi malami ne. Kar mu manta, Sheikh Jafar ba kawai a kan husufi ya nuna rashin fahimtarsa ta kimiyya ba, domin a wasu wuraren akwai inda ya ke cewa idan da duniya na kewaye da sai a ga masallacinsa da ke Gadon Kaya, a yammacin Kano ya karkata wajajen Tarauni da ke gabashin Kano (Fahimta wadda ya kwafo kwabo-da-kwabo da bayanin da Sheikh Bn Baz ya yi a Masallacin annabi inda ya ke bada karatu). Wannan ilimi kuma na juyawar duniya a fili ya ke, kuma daya daga cikin hujjojinsa na zahiri shine, a yayin da Malam Lawan Triump ke sallar azahar a masallacinsa, a harami ko masallacin madina la’asar a ke yi. Da duniya bata juyawa da dukkanmu lokaci guda za mu yi sallah. Amma kowa ya sani cewa akwai zangogin lokaci guda sha biyu a duniya. Sanda wani ke tashi daga barci, sannan wani zai kwanta.

Malam Lawan, ya ci gaba da cewa wai zancen da na kawo na kafawa Jafar Hujja ba Nazari na ba ne kawai ji-ka-karar ne na ji a gari na kwafo, sannan da cewar kuma hira aka yi da ni a radio. To ya sani cewa ba hira ba ce, shiri ne da nake gabatarwa duk mako a kan kimiyya da Qur’ani. A daidai wancan lokacin, na shekara goma da barin Jami’ar Bayero inda na karanta Hausa da Islamic Studies. Na rubuta littafi na na farko (a 2005), an buga shi akan addinin musulunci da kimiyya (me suna Asalin Halitta da Rayuwa) wanda gwamnatin Kano ta siya ta rarrabawa makarantun sakandare da ke fadin jihar Kano. Kuma nima din kamar Sheikh Jafar, gidan karatun Allon ne ya haife ni kuma na je jami’a. Sannan daya daga cikin Jami’o’in da ake ji da su a duniya har gobe, Cambridge University, ta bani gayyata zuwa England yin kwas saboda rubutun da nake duk mako a jaridar leadership tun 2006 a kan kimiyya da addini. Haka nan gidajen rediyon BBC, VOA da TRT dukkansu na kira na domin amsa tambayoyi da bayani a kan ilimin sarari samaniya banda kafafen watsa labarai na cikin gida. Na yi wa BBC shiri na musamman akan husufi. To amma shi Malam Lawan bai san duk wannan ba, domin da alama ba ya bincike yadda ya kamata idan ya tashi raddi.

A karshe zan ja hankalinmu gaba daya, walau malamai, masu ilimi, marasa ilimi har da jahilai. Mu sani cewa shi ilimi a muhallinsa na ilimi, abubuwa biyu basa riskarsa, wato na farko tsufa, ilimi bai taba tsufa ba domin ilimin da aka sani shekaru dubbai a baya, sabo ne ful ga wanda ya san shi yanzu. Sannan ilimi baya raguwa sai dai ya karu. A jumlace, Dan Adam ba zai iya sanin dukkan ilimi ba, kuma a kullum muka kara ilimi, sai jahilcinmu ya kara bayyana, kamar yadda Allah ya ce mana; Q31:27 “Kuma da abinda ke cikin kasa duka na itace sun zama alkaluma, Kuma teku ta na yi masa tawada, sannan a kara da wasu tekunan bakwai, kalmomin Allah ba za su kare ba.”

Haka nan babu wani Dan Adam tun daga farkon mutane zuwa karshen zamani, wanda za a ce ya san dukkan ilimi, kowa sai dai ya yi iyo iya inda Allah ya ba shi dama. Dalilin da Allah ya umarci manzo kansa da da ya ce; Q20:113 “Kuma ka ce “Ya Ubangiji ka Kara min ilimi.”

Wato ba’a koshi da ilimi, shi ya sa Allah ya ce da Annabi ya lazimci wannan addua. To idan har masu munajati da ubangiji, wadanda ke iya tambaya kai tsaye a basu amsa, an umarce su da su yi haka, Ina ga mu yan-ku-ci-ku-bamu?
Sannan duk zurfin iliminka, daga ranar da kake jin cewa lallai ka tumbatsa kuma ka san komai, daga ranar ka zama jahili. Domin da zarar ka ji irin haka, to kai dai ilimi kun yi hannun riga. Dole a duk matsayin da ka kai na ilimi, ka kasance mai kankan da kai ka nemi dadi, kamar yadda Allah ya cewa Annabi. Wanda duk ya ji izza a ilimi hakika jahilci ya zamar masa aboki. Mun ga misalin da Allah ya bamu a suratul Kahfi inda Annabi Musa, Ulul A’azam kuma annabin zamanin sa mai littafi wanda Allah ke magana da shi, amma da ya ji ya tumbatsa a ilimi sai Allah ya tura shi wajen Khidir domin jahilcinsa ya bayyana a gare shi.

Akasarin musulmi a yau sun karkasu kungiya-kungiya, kowacce ta binne kanta a akwatin akidar ta, kuma ta na ganin cewa ta tumbatsa a iliminta, sai dai su bi Salaf dinsu kawai, don haka sai su ka kasance tsaye cak a iya inda su ka tsaida kawunansu, ilimi da zamani ya zo ya wuce ya barsu a baya. Shi yasa Malamai irinsu Lawan Triumph ba sa bani mamaki, domin kowa na ganin yadda su ka maida mimbarorinsu tamkar teburin mai shayi, a kwaso zantuka babu hujja sannan kuma mimbarin kanfen din lalatattun yan siyasa. To, shi kifi idan ya na cikin rijiya, gani ya ke iyakar duniya ta kare a wannan rijiya, ba sauran komai a duniya. Alhamdulillah domin Annabi dai cikin Hadisin Bukhari 3482 ya ce “Idan ba ka jin kunya, ka aikata abinda ka ga dama.”

Zan rufe da zancen hikima na larabawa wanda ya kasa mutane zuwa azuzuwa hudu;

1. Wanda bai sani ba, Kuma bai san cewa bai sani ba…Jahili ne a kaurace masa.
2. Wanda bai sani ba, Amma ya san bai sani ba…Dalibi ne, a sanar da shi.

3. Wanda ya sani, Amma bai san ya sani ba…Mai barci ne a tashe shi.

4. Wanda ya sani, Kuma ya san ya sani…wannan Malami ne a bi shi.

Rabbit Zidni ilma… Jummu’a Mubarak ’Yan Uwa.

Malam Ali manazaci kuma marubuci a Kano

By ukarofi