Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya isa hedikwatar hukumar da ke Abuja, Babban Birnin Tarayya, a ranar Alhamis domin karɓar ragamar shugabanci bayan rantsar da shi da aka yi a Fadar Shugaban ƙasa.
Rantsarwar, wadda Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a ɗakin taro na Fadar Shugaban ƙasa (Council Chamber, Aso Rock), ta zo ne bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon shugaban hukumar.
Farfesa Amupitan, wanda malami ne na dokoki a Jami’ar Jos (UNIJOS), ya fito ne daga garin Ayetoro Gbede da ke ƙaramar Hukumar Ijumu a Jihar Kogi. An ba shi lambar girmamawa ta SAN (Senior Advocate of Nigeria) a shekarar 2014, kuma ya kware a fannonin dokar kamfanoni, shaidar shari’a, da tsarin gudanarwar kamfanoni da keɓance harkokin gwamnati.
Tare da shiga ofis ɗin nasa, Farfesa Amupitan zai kula da shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka tsara a watan Nuwamba 2025, da kuma zaɓen ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya (FCT Area Council election) da ke tafe a watan Fabrairu 2026.
A lokacin da yake isa ofis ɗinsa, an tarbe shi da jajayen kyallaye da maraba daga manyan jami’an hukumar, inda ya yi jawabi mai cike da kwarin gwiwa, yana mai cewa zai tabbatar da gaskiya, adalci da sahihancin tsarin zaɓe.
Ya ce, “Za mu gina tsarin da zai dawo da cikakken amincewar ‘yan Nijeriya ga zaɓe. A ƙarƙashin jagorancina, INEC za ta kasance hukumar da ke kare muradun jama’a, ba ta kowa ba.”
