Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zaɓe a Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin ƙasar a matakin tarayya.
Akpabio, wanda aka zaɓe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin karatu na biyu a kan dokar gyaran tsarin zaɓe a zaman majalisa da aka yi a ranar Laraba.
“Ina da tabbacin cewa ni da Sanata Abaribe, wanda muka shafe kusan shekaru 25 muna cikin harkar siyasa, na san ba mu damu da jam’iyya ba, ana iya lashe zaɓe a ko’ina.
“Ka na da ƙwarewa sosai, amma za ka yarda da ni cewa tun bayan faɗuwar PDP, zaɓe ya inganta matuƙa a wannan ƙasa.
“Na tuna, ina da kusanci da yawancin shugabannin ƙasa tun daga 1999, kuma a 2007 lokacin da na ci zaɓe a matsayin gwamna, shugaban ƙasa na lokacin, Allah ya jiƙansa, Shugaba Yar’Adua, ya fito fili ya ce zaɓen da ya kawo shi mulki yana da lam’a.
“Ya ce cike yake da kura-kurai da maguɗi. Tun daga lokacin, muka fara rufe guraben da ke haifar da matsala.”
Akpabio ya ƙara da cewa duk da cewa ’yan Nijeriya na fuskantar ƙalubale, tsarin ya inganta.
“Ka duba zaɓen da ya gabata, har sai da muka je Kotun ƙoli muna muhawara kan ko lashe babban birnin tarayya kadai ya isa ya sa dan takara ya zama shugaban ƙasa,” inji shi.
“Hankali kawai ya isa ya gaya mana cewa ba haka dokar zabe take nufi ba,” inji Akpabio.
Shugaban majalisar dattawa ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki bayan PDP ta fadi zabe a shekarar 2015.
Ya tsaya takarar Sanata a 2019 a karkashin jam’iyyar APC, amma bai ci ba.
Sai dai tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi minista daga bisani, kafin a 2023 kuma ya ci zaɓen sanatan daga jiharsa ta Akwa Ibom, sannan aka zaɓe shi shugabancin majalisar.
