Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kimanin ‘ya’yan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) 500 ne daga ƙananan hukumomin Fagge da Ungogo a jihar Kano suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Manajan Daraktan Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jam’are, Rabiu Bichi, ya karvi waɗanda suka sauya sheƙa a ranar Laraba.
Ya ce matakin nasu ya nuna yadda ake samun ƙwarin gwiwa a kan shugabancin shugaban kasa Bola Tinubu da kuma manufofin ci gaban APC.
Mista Bichi ya bayyana cewa manufofin jam’iyyar APC na ci gaba na jan hankalin ‘yan Nijeriya, inda ya bayyana ficewar wasu Gwamnoni a matsayin wata alama ta ƙarfin jam’iyyar.
Ya kuma baiwa sabbin ‘ya’yan jam’iyyar tabbacin samun dama da kuma shigarsu cikin jam’iyyar APC, yana mai cewa babu wani ɗan jam’iyyar da za a mayar da shi saniyar ware.
Bichi ya bayyana manufofin gwamnatin APC mai hangen nesa kan samar da abinci da bunƙasar tattalin arziki, inda ya jaddada cewa dabarun noman rani na zamani na Kogin Hadejia-Jam’are sun yi daidai da tsarin samar da abinci na Tinubu.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, wanda shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya wakilta, ya yaba wa waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC.
Shugaban jam’iyyar APC na Kano ta tsakiya, Shehu Ungogo, ya ce manufofin Tinubu sun ƙara havaka tattalin arzikin Nijeriya, tare da dawo da ƙwarin gwiwar jama’a ga APC.
Masu sauya sheƙar sun bayyana irin ci gaban da jam’iyyar APC ta samu da kuma jajircewar inganta rayuwar ‘yan Nijeriya a matsayin dalilan tafiyarsu.
