Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kungiyar wayar da kai da horar da matasa a fannin fasahar zamani ta ƙirƙira ta yanar gizo (intanet), wacce ke ba wa matasa damar samun aikin yi, wato Hedera Network Developer Course da ke jihar Kano tare da haɗin gwiwar Dar Blockchain, sun shirya taron wayar da kai ga matasan Kano kan yadda za su koyi wannan fasaha domin cin gajiyarta wacce za ta basu damar samun aikin yi da cigaban tattalin arziƙi ga kansu da ƙasar su Nijeriya.
A cewar Barista Abdulhadi Isah Ibrahim, shugaban Sihaad Organization, ya bayyana hakan ne a lokacin taron da aka gudanar a gidan Mambayya na Tunawa da Malam Aminu Kano, da ke unguwar Gwammaja, Kano, a makon da ya gabata.
Har ila yau, wannan fasaha ta samo asali daga ƙasar Amurka a shekara ta 2020, kuma ita ce tushen ƙirƙirar abubuwan da suka shafi samar da fasahar kuɗin zamani da ake kira Coins. Wannan horo yana taimaka wa matasa wajen samar da hanyoyin tattara bayanai kamar na ilimi, lafiya, tarihi, takardun makaranta, da sauransu.
Shi ma shugaban wannan ƙungiya na Nijeriya da Afirka baki ɗaya, Injiniya Ibrahim Aliyu S. Kamina, ƙwararre a fannin tsaron fasahar sadarwa kuma shugaban Kaminova Global, ya bayyana cewa taron yana da matuƙar muhimmanci ga matasa da al’ummar Nijeriya.
Ya ƙara da cewa abin takaici ne yadda aka samu wani ɗan Nijeriya mazaunin Legas ya yi kutse cikin hanyar sadarwa ta Email da ke ofishin shugaban ƙasar Amurka har ya yi damfara da kuɗi sama da miliyan 500. Ya ce Nijeriya ce ta uku a duniya wajen irin wannan laifi bayan Indiya da China. Saboda haka, irin wannan taro na wayar da kai ne hanya mafi kyau ta kawar da ayyukan masu damfara a yanar gizo.
