Tsakanin Masussuka da Rijiyar Lemo a kan ‘la taƙribu’

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ 

Wato na kalli wani video inda Sheikh Rijiyar Lemo ke yi wa masu da’awar Qurani zalla kalubale kan fassararsu ta ayar cikin Baƙara wadda ta yi hani ga mazaje kada su kusanci mata masu haila. Ya kawo ayar Q2:222 ‘Wala taƙrubuhunna hatta yad hurna.”

Wato kada ku kusance su har sai sun yi tsarki. Inda ya ci gaba da bayanin cewa a fahimtarsa ba wani Dan kala-kato Mai bin Qurani zalla da zai iya fassara ma’anar wannan aya da wata ayar ta Qur’ani, sai dai ya yi fassara kawai ta sa ta kansa. Sai dai ya nisance ta, ya kaurace mata sannan ya nisanta ta da sauran mutane. Haka ne kawai aiki da Qur’ani zalla. Kuma ya san babu wani mahaukacin Dan kala-kato da zai ce ya kauracewa matarsa haka.

Shi kuma Masussuka da ya tashi yi masa raddi sai ya ce Rijiyar Lemo bai ma fahimci Qurani ba kwata-kwata, domin da ya fahimci Qurani da ba zai jeho kalubalen a kawo ayar da ta fassara wannan ba, saboda akwai ta. A nan Musussuka ya kawo ayar Suratul Israh wadda ta ce; Q17:34 “Wala taƙribul malal yatimi.’

Wato kada ku kusanci dukiyar marayu. A na sa bayanin sai ya ke cewa to shin a nan ma haka za’a fassara Wala taƙribul din da cewa tunda an ce kada a kusanci dukiyar marayu sai a yi amfani da irin waccan fahimtar ta Rijiyar Lemo a nesanta dukiyar a kaita a watsar?

To irin wannan amfani da tunani da yin tudabburin ayoyi shi yasa Masussuka ke samun magoya baya a kullum saboda ya na appealing to sensibilities na, musamman, matasa.

Kullum dai mu kiran da muke yi a shine a girmama ikon ra’ayi da Allah ya baiwa kowa, sannan a dawo kan ginshikin wa’azi wanda Allah ya shimfida ga ma wadanda ba musulmi ba, ballantana a junan mu, yadda duk yadda mu kai da banbanci, lallai akwai inda mu ka hadu babu jayayya.

Q16:125 “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.”

Kaucewa wa wannan tsari ne ya jawo mu ke a halin da muke ciki. A jiya nayi posting kan hadarin musulmi ya rika cewa “God is dead” sai wani yaro wanda daga dukkan alamu watakila Mulhidi ne. Sai ya garzayo da tunanin zai fusata ni, sai ya ce “Ya maimaita din, God is dead, kuma har daga cikin zuciyarsa”. Sai na ce masa to sai me? Yayi ta kwala ihu ya na fada idan don ta nine, in ya so ma ya zama tamkar shaka da fitar numfashinsa, domin ba domin irinsu na yi posting ba. Shikenan ya yi ƙus.

Saboda tuni Allah ya nuna mana yadda ya tarbiyanyar da Annabi da ya cewa kafiran Makka “Lakum dinikum wa liyadeen” Wato idan mutum akuya ya daure ya ce ita ce Allah, ruwansa ne. Aikin Manzo (da mu da zamu kwaikwaye shi) bai wuce; Q38:70 “Ba a yi min wahayin komai ba face cewa ni mai gargadi kawai ne, mai bayyanawa.”

Aikin ke nan, wanda ya ji ya karba, to don kan sa, wanda kuma ya ki karba shi ma dai domin kansa ba ruwanka. Kamar yadda cikakken bayanin ya zo a ayoyin; Q22:49-51 “Ka ce: “Ya ku mutãne! Nĩ wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa. To, waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, sunã da gãfara da arziki na karimci. Kuma waɗanda suka yi aikin ɓãtãwa a cikin ayõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗancan ‘yan Jahĩm ne.”

Malam Ali manazarci ne a Kano

By ukarofi