Atiku fa ya makara

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Atiku Abubakar bai taba samun damar zama shugaban kasa a Najeriya ba irin a shekarar 2023 saboda irin kamun ludayin mulkin Buhari da APC, wanda ya rugurguza kusan kowanne fanni na zamantakewar Najeriya, kama daga siyasa, tattalin arziki, tsaro da cin hanci da rashawa.

Najeriya ta ciri tutar zama kasa mafi yawan matalauta, yankin Arewa ya zama daya daga cikin mafi rashin tsaro da talauci a duniya, sannan daf da zabe, tsarin canza Naira da wata sabuwa ya haifar da kunci mafi muni a tarihin kasar. Duk da irin mahaukatan kudaden shiga da gwamnatin Buhari ta samu da na bashi wanda ya kai dala biliyan $312, babu wani aiki kwaya daya na dala biliyan $5 da gwamnatin ta aiwatar, ta kammala, har ta kaddamar a shekaru takwas. Cin hanci da rashawa ya yi katutu da ba’a taba ganin irinsa ba, yayin da Buhari ya rushe tsarin yaki da cin hancin wajen tabbatar da Emefele ci gaba da zama a kujerar Gwamna na babban banking kasa, bayan munanan zarge-zarge (Wanda a yanzu ake maganar ya dawo da Tiriliyan 4), da kuma daurewa masu cin hancin gindi ta hanyar sako Jolly Nyame da Joshua Dariye daga kurkuku.

Gungun wadannan matsaloli ya sa akasarin mutane sun dawo daga rakiyar APC kuma su ka kudiri aniyar kada ita a zaben 2023. Dalilin da ya sa Atiku bai taba samun damar cin zabe a ruwan sanyi ba irin a wannan lokaci. Amma kash! Atiku ya cuci kansa, ya cuci yan Najeriya wajen barin wannan dama ta kubce masa. Domin Atiku da kansa ya kayar da kansa a wannan zabe. Dalili kuwa shine a tarihin zabe a duniya ba’a taba samun inda aka yi irin wautar da aka yi a zaben 2023 ba. Domin gungun yan adawa sun sami jumillar kuri’u miliyan 14 da doriya (Atiku 6.9, Obi 6.3, Kwannkwaso 1.1), amma ta zama kuri’ar banza yayin da Tinubu ya lashe zaben da kuri’a miliyan 8, duk da tazarar kuri’a miliyan shida ta Yan Adawa.

Me ya kada Atiku? Na farko dai a 2019 ya tsaya takara a jam’iyyar PDP tare da Peter Obi a matsayin mataimakinsa, amma ya bari Obi ya balle ya tsaya takararsa a wata jam’iyya daban, wato Atiku ya bar kuri’a miliyan 6 ta kauce masa salun-alun. Sannan bayan zama Dan takara ya yi watsi da bukatar wanda ya zo masa na biyu a zaben cikin gida, wato Wike. Duk wanda ya san tsarin PDP ya san cewa su na da wata yarjejeniya cewa idan Dan takara ya fito daga kudu dole shugaban jam’iyyar ya kasance Dan Arewa haka idan daga Arewa Dan takara ya ke, to dole shugaban jam’iyyar ya kasance daga kudu. Atiku yayi fatali da bukatar su Wike domin a cire Iyorchia Ayu daga shugaban jam’iyya a baiwa ɗan Kudu.

Wannan blunders guda biyu ita ta kayar da Atiku a zaben 2023 saboda ya kewaye kansa da Yan siyasa marasa capacity a kusa da shi da kwakwalensu ba sa iya dogon lissafi. Sannan shi kansa Atiku idan ka Kalli mu’amalar sa a siyasance tun daga 2003, ya fi kama da basaraken gargajiya fiye da Dan siyasa. Akwai wani Sanata da muke hira da shi ya ce min tun 2003 ya gane cewa Atiku zai wahala ya zama shugaban kasa. Dalili kuwa shine a wancan lokacin Gwamnonin kasar akasari na goyon bayansa ya tsaya takara, kuma sun taru a gidansa ana meeting sai Obasanjo ya shigo su ka kebe, inda aka ce har dubale yayi wa Atiku domin ya janye bukatar sa. Ba tare da dawowa ya yi shawara da Gwamnoni da sanatoci da ke wajen ba sai kawai ya sauko ya ce musu sun daidaita da Obasanjo kuma ya janye masa.

A tarihin siyasar Najeriya ba’a taba Dan siyasa me amfani da basira da shiri da juriya irin Tinubu ba. Munga yadda Buhari ya shiga zabe karo uku ya na faduwa saboda bai sami ginshikan cin zabe ba har sai da yayi hadaka da Tinubu. Shi zabe strategy ne cinsa da amfani da basira. Tinubu ya ga yadda ya sha da kyar a zaben 2023 don haka ya gane cewar sakaci da sakarcin yan adawa ne ya bashi kujerar, don haka ya na shigowa gwamnati ya maida hankalinsa wajen tabbatar da cewa ya kassara adawa a Najeriya ta hanyar saka PDP a aljihu ta yin amfani da Wike. Ya bashi minista mai matukar tasiri yadda zai iya ci gaba da rike jam’iyyar PDP yadda za ta ci gaba da yiwa APC aiki.

A yadda Tinubu ya kassara Adawa, kuma a bayyane ya ke cewa Atiku ne ya bada gudunmuwa wajen karya PDP sakamakon kin amincewa da bukatar su Wike, bukatar da a banza a wofi bayan wata shida da faduwar zabe Ayun ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar. Karin kuskure shine, maimakon Atiku ya tsaya ya kwaci PDP sai ya gwammace ficewa. To, a shekaru kasa da biyu ya ke tsammanin zai gina ADC ta zama jam’iyyar adawa da za ta iya ja da APC? Da alama dai, baki, da wancan sanata ya yiwa Atiku zai tabbata na cewa ba zai taba mulkar Najeriya ba. Kuma alamu sun nuna haka tunda ya kasa a 2023, me kake tsammani zai iya yi a 2027?

APC ta tara mahaukatan kudade, ta fito da tsaruka na bada tallafi a fannonin kanana masana’antu, gwamnoninta na da kudade masu nauyi wanda za su fito a nemi kuri’a. Ta ina Atiku zai iya ja da su? Maganar gaskiya Atiku ya cuci kansa a baya, ya kuma kashewa yan Najeriya damar kawar da mulkin APC tun a 2023. A yanzu shi kadai da wasu Yan tsiraru ba tare da wata cikakkiyar jam’iyyar adawa ba, ku gane min ta inda zai iya kwatar mulki a hannun APC da Tinubu?

APC ta kassara Najeriya, daga kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka ta dawo ta hudu a bayan South Africa, Egypt da Algeria. Sannan ba’a taba samun kudi tun daga 1999 zuwa yanzu ba, irin daga farkon lokacin Buhari zuwa yanzu. A wannan shekaru goma an sami kudade da suka haura $500 billion amma babu abin a zo a gani a kasa, idan banda karuwar talauci da rashin tsaro. Duk manyan birane idan ka shiga sai manya manya gine gine da manya manyan motoci na Yan siyasa ke yawo yayin da abinci ya gagari talaka. Tinubu ya karfafa elites, ya dada talauta yan Najeriya. Babban takaicin kuma shine, babu wani wanda za ka kalla a yau a ce zai iya ceto Najeriya daga halin da take ciki. To, a wannan yanayi, ku gaya min abinda zai hana Tinubu zarcewa a 2027? Idan banda wani Iko na Allah.

Ali Abubakar manazarci kan harkoki na yau da kullum

By ukarofi