
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An zargi jami’an rundunar ƴan sanda da cin zarafi da sake kama ɗan gwagwarmayar Omoyele Sowore a harabar Kotun Majestare ta Kuje da ke Abuja, inda suka tilasta masa shiga wata mota duk da an bada belinsa.
Shaidun gani da ido sun ce al’amarin ya auku ne jim-kaɗan bayan da kotun ta bada belin Sowore da wasu mutane 13.
A cewar Sahara Reporters, a yayin da lauyoyi ke shirye-shiryen takardun sallamarsu, jami’an ƴan sanda ƙarƙashin jagorancin jami’in bincike (IPO), CSP Ilyasu Barau na ofishin DC-CID na Abuja, ya naushi Sowore tare sannan ya jefa shi cikin motar ƴan sanda.
Wani shaida ya bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya nuna jarumta a lokacin da ƴan sandan suke ƙoƙarin fita da shi ba tare da wani bayani ba.
