
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya naɗa yayansa Alhaji Adamu Mohammed a matsayin Sarkin sabuwar Masarautar Duguri da aka samar a jihar.
An tabbatar da naɗin ne a yau Juma’a, yayin miƙa wa Sarkin takardar naɗin da aka masa a Fadar Masarautar da ke Duguri.
Da yake jawabi, Sakataren gwamnatin jihar, Aminu Hammayo ya kirayi sabon sarkin da ya cigaba da taimaka wa tsare-tsaren gwamnatin jihar da shirye-shiryen inganta al’umma da ci-gaba mai ɗorewa.
Shi ma basaraken a nasa ɓangaren, ya bayyana cewa ya ba Gwamna Bala muƙamin sarauta na ‘Yariman Duguri’.
Ya kuma miƙa godiyarsa ga gwamnan bisa karramawar da ya masa, yana mai addu’ar Allah ya saka masa da alkhairi.
Kazalika, ya yi alƙawarin yin aiki tare da sauran masu riƙe da muƙaman sarauta a jihar wajen inganta harkokin zaman lafiya, haɗin kai da cigaba mai ɗorewa.
