Zubar da ciki: An sake yamutsa hazo tsakanin Akpabio da Natasha a zaman Majalisar Dattawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Talatar da ta gabata ne aka samu rashin jituwa a Majalisar Dattawa yayin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, da Sanata Adams Oshiomhole suka fafata tare da taƙaddama akan ƙudirin gyaran dokar aikata laifuka da ke neman tsananta hukunci ga masu taimakawa wajen zubar da ciki a cikin Kundin Dokar Laifuka (gyara) 2025.

Tun da farko a zaman majalisar dattijai bakiɗaya, ta zartar da wani muhimmin ƙudiri na doka ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da ƙaramar yarinya, ba tare da zaɓin tara ba.

Babban zauren majalisar ya ce hukuncin mai tsauri ya zama dole don daƙile masu laifi da kuma kare yara daga cin zarafinsu, wanda ta bayyana a matsayin “mummunan laifi da ke iya lalata rayuwar yara har abada”.

ƙudirin, wanda ya samo asali daga majalisar wakilai kuma aka aika zuwa majalisar dattijai don daidaitawa, yana neman yin kwaskwarima ga wasu tanade-tanade na kundin laifuffuka na ƙasar don magance abubuwan da ke faruwa a wannan zamani.

Yayin zaman majalisar, ‘yan majalisar sun kaɗa ƙuri’a baki ɗaya don amincewa da hukuncin daurin rai da rai kan laifin kazanta, wanda a halin yanzu yana da hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda ya jagoranci zaman, ya ce: “Lalata ya ma fi fyaɗe.

“Wannan lamari ne mai matuƙar muhimmanci kuma ya kamata a ɗauki hukunci mafi tsauri. Duk wani lalata da aka yi wa ƙaramar yarinya a Nijeriya daga yanzu yana jawo ɗaurin rai da rai. Kowa ya sani.”

Majalisar dattawan ta kuma ƙara da hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari na fyaɗe da sauran nau’o’in jima’i na tilas, wanda ya shafi maza ko mata.

A cikin sabon ƙudirin, Sashe na 2 (1), ya ce, “Duk mutumin da ya tsare namiji ko mace, yarinya ko mace ba tare da son ransa ba a kowane wuri domin ya samu ilimin canal ba bisa ƙa’ida ba; a gidan karuwai ko kuma a ko’ina, ya aikata babban laifi kuma ya kai mafi ƙarancin shekaru 10 a gidan yari, bisa ga laifinsa.”

Bayan zazzafar tattaunawa da kuma yin la’akari da batun zubar da ciki da ya shafi addini, bisa la’akari da buƙatar ƙarin haske kan wasu tanade-tanade, daga ƙarshe majalisar ta janye yin nazari kan ƙudirin, inda ta miƙa shi ga kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin shari’a da kare haƙƙin bil’adama domin ci gaba da nazari kan rahoton nan da makonni biyu.

Sai dai bayan an dakatar da batun, Sanata Natasha ta nemi damar yin magana tana mai cewa batun ya shafi mata kai tsaye, amma Akpabio ya hana ta magana, yana mai cewa an rufe muhawarar gaba ɗaya.

Sanata Adams Oshiomhole ya goyi bayan matakin Akpabio, yana cewa sake buɗe batun zai karya dokokin majalisar.

Bayan zaman, Natasha ta bayyana takaici cewa an hana ta yin magana kan batu da ya shafi haƙƙin mata da lafiyarsu, tana mai cewa za ta bayar da gudunmawa lokacin da kwamitin majalisar zai sake nazarin ƙudirin.

Bayan wani lokaci, Akpabio ya kira Sanata Natasha sau da yawa, yana mai cewa, “Mai girma Sanata, an dakatar batun, amma idan kana da wani abu da za ka ƙara, za ka iya.”

Yayin da ta fara magana, inda ta jaddada cewa damuwarta ya shafi batun zubar da ciki ne, Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya katse maganar, inda ya ƙara da cewa dokokin majalisar sun hana sake duba batutuwan da aka riga aka yanke hukunci a kansu.

Oshiomhole ya kara da cewa, “Idan har aka yi watsi da wani al’amari kuma aka yanke hukunci a kai, to ba zai yiwu a sake buɗe shi ba,” inji Oshiomhole, yana mai kira ga abokin aikin sa da ya mutunta dokokin.

A martanin da ya mayar, Akpabio ya amince da maganar Oshiomhole, inda ya ce, “Ni ba ruhun da zai iya sanin abin da take son faɗa ba ne,” amma ya kara tabbatar da cewa tsarin majalisar dattawa ba ya damar tattaunawa kan lamarin da zarar an yanke hukunci. Daga nan ya yi mulkin Sanata Natasha ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan na zuwa ne kawai makonni biyu bayan Natasha ta koma majalisar dattawa bayan dakatarwar da ta yi na tsawon watanni shida.

An dakatar da ita ne a watan Maris din da ta gabata, bisa zargin ta da karya ƙa’idojin Majalisar Dattawa, matakin da ya janyo kakkausar suka daga ƙungiyoyin farar hula da ‘yan siyasar adawa, duk da cewa Majalisar ta kare matakin da ta ɗauka.

Daga baya sanatar ta PDP ta kai ƙara kotu a watan Yuli amma ta kasa samun umarnin komawa. Bayan ta kammala dakatarwar da aka yi mata na watanni shida a watan Satumba, ta rubuta wa majalisar dattawa a hukumance inda ta bayyana aniyar ta na komawa.

Majalisar dattawan, a ranar 23 ga watan Satumba, ta bankaɗo ofishinta, wanda ya shafe watanni shida a kulle, wanda daga baya aka ba ta damar komawa ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da majalisar ta koma bakin aiki.

By ukarofi