Rayuwar Kwankwaso na cigaba da amfanar da al’umma a faɗin duniya — Dr. Shitu Marafa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Daya daga cikin manyan jagororin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) daga ƙananan hukumomin Gaya, Albasu da Ajingi, Hon. Dr. Shitu Marafa Gaya, ya bayyana rayuwar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin mai albarka wadda ta ci gaba da amfanar da miliyoyin jama’a a Jihar Kano da ma duniya baki ɗaya.

Dr. Marafa ya bayyana hakan ne a cikin saƙon taya murna da ya aika wa Jagoran Kwankwasiyya na duniya, inda ya yaba wa jajircewarsa da hidimarsa ga al’umma.

Ya ce rayuwar Sanata Kwankwaso ta kasance abin koyi ga mutane da dama saboda jajircewarsa wajen ilimi, ci gaban al’umma da walwalar jama’a.

“Jagorancin hangen nesa na Sanata Kwankwaso ne ya gina tushen ci gaba a Jihar Kano,” inji Marafa. 

“Wannan ne ya bai wa Maigirma Gwamna Abba Kabir Yusuf damar ci gaba daga inda Madugu ya tsaya wajen gudanar da ayyukan alheri da na ci gaban jama’a.”

Dr. Marafa ya ƙara da cewa yana fatan irin wannan gado da Sanata Kwankwaso ya kafa zai ci gaba da amfani ga al’umma har tsawon lokaci.

“A gaskiya, Sanata Kwankwaso kansa ba ya san adadin daliban da suka amfana da tallafin ilimi na sa, ko kuma wadanda suka samu jari da taimakon lafiya ta dalilinsa,” inji shi.

A ƙarshe, Dr. Marafa ya taya Sanata Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 69, tare da addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, tsawon rai da albarka mai yawa.

By ukarofi