
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda ya ƙi amince wa buƙatar ba tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i damar zama magajinsa a kargar mulki a shekarar 2007.
Da fari, El-Rufa’i a gwamnatin Obasanjo zango na biyu, ya riƙe muƙamin Darakta Janar na Hukumar Kula da Tsare-tsaren Kadarorin Gwamnati (BPE) kana daga bisani ya zama ministan Abuja.
A yayin barin karagar mulki a 2007, Obasanjo ya zaɓi Marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar’Adua a matsayin magajinsa.
Da yake jawabi a Abeokuta, Babban Birnin Jihar Ogun a taron shekara-shekara na ƙungiyar Ajibosin mai taken ‘Importance of Leadership in Governance’ a jiya Juma’a, Obasanjo ya ce tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka ya shawarce shi da ya ɗauki El-Rufa’i a matsayin wanda zai gaje shi, amma ya yi buris da hakan.
Shi ma Chidoka, a jawabinsa na taron ya tunatar da lokacin da El-Rufa’i ya bada sunansa ga Obasanjo a lokacin da yake ɗan shekara 34, lamarin da ya ƙara kusanto da shi Fadar Shugaban Ƙasa da kuma zama Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra FRSC.
Obasanjo ya bayyana cewa, ya yi watsi da buƙatar ɗaukar El-Rufa’i a matsayin magajin ne saboda ya lura akwai buƙatar a ba shi lokaci domin ya ƙara gogewa ta fuskar siyasa.
