INEC ta ƙaddamar da fasahar AI don inganta ayyuka yayin tunkarar zaɓen Anambara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ƙaddamar da sabuwar na’urar fasahar AI domin inganta ayyukan ma’aikata da kimtsi cikin lokaci yayin da ake tunkarar zaɓen Jihar Anambara da za a yi a ranar 8 ga watan Nuwamba.

An yi wa na’urar laƙabi da INEC Training Virtual Assistant’ ko kuma ‘INECTrainingBot’, wanda aka gabatar da ita a jiya Juma’a, wadda za a iya samu ta manhajar Telegram.

A cewar hukumar zaɓen, na’urar za ta riƙa bada damar samun baki ɗaya kayayyakin zaɓe ga ma’aikata cikin sa’o’i 24, horo na bada damar tattaunawa da ababen koyo da ka iya bijirowa domin samun damar ɗaukar darussan zaɓe daga kowane wajen mutum yake.

INEC ta ƙara da cewa, samar da hakan wani ɓangare ne na faɗaɗa hanyoyin amfani da fasaha wajen inganta ayyukan kayayyakin zaɓe da jami’ai a yayin zaɓuka.

A wata sanarwa kafar X, INEC ta ce za ta fara aikin tantance masu zaɓe a Anambara a ranar 25 ga watan Oktoba a mazaɓun sanatoci uku na jihar.

By Babaji