Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya karɓi sabon Kwamandan hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) da aka tura domin jagorantar rundunar a Jihar Kano.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.
Yayin ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan a fadar gwamnatin Kano, sabon kwamandan, Bala Bawa Bodinga, ya yi alƙawarin yin aiki tare da gwamnatin Kano domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
Kwamanda Bodinga ya tabbatar da biyayyarsa da cikakken goyon bayan sa wajen gudanar da aikin tsaro na jiharsu, yana mai cewa:
“Zan yi aiki tare da Gwamnatin Kano, kuma ba zan bari wata ƙungiya ko wasu ƙarfi daga wajen nan su kawo matsala ko su sa ni na saɓawa gwamnati ba.”
Ya kuma jaddada aniyarsa ta inganta ƙwarewar jami’ansa da ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro domin samar da zaman lafiya a Kano.
A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarbi sabon kwamandan tare da tabbatar masa da cikakkiyar haɗin kai da tallafi daga gwamnatin Kano domin ganin ya yi nasara a aikinsa.
Gwamnan ya tabbatar da himmar gwamnatinsa wajen ci gaba da inganta tsaro, kare rayuka da dukiya, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin dukkan hukumomin tsaro a jihar.
Gwamna Yusuf ya kuma yabawa hukumar Civil Defence bisa rawar da take takawa wajen kare muhimman kadarorin ƙasa da raya tsaro a cikin al’umma, yana mai nanata cewa Kano za ta ci gaba da bai wa dukkan hukumomin tsaro damar gudanar da ayyukansu ba tare da tangarɗa ba.
