Kwamandan NSCDC ya miƙa ta’aziyya kan rasuwar kwamishinan tsaron cikin gida na Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen Jihar Gombe, Kwamanda Jibrin Idris, ya bayyana babban jimami bisa rasuwar kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Gombe, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (Mai Ritaya), tare da ɗan sandan da ke tsaron sa, Sajan Adamu Husaini, da direbansu, waɗanda suka rasu sakamakon mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a ranar Juma’a.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Buhari Sa’ad, ya fitar, Kwamanda Idris ya bayyana cewa wannan lamari babban rashi ne ba kawai ga iyalan mamatan ba, har ma ga Gwamnatin Jihar Gombe da al’ummar jihar baki ɗaya.

Kwamandan ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da iyalan mamatan da abokansu, inda ya jaddada cewa mamatan sun bayar da gudunmawa mai muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

“Kwamandan ya yaba da irin jajircewa da sadaukarwar da Laftanar Kanar Abdullahi Bello (Rtd), Sajan Adamu Husaini da direbansu suka nuna wajen hidima ga jihar Gombe.

Rasuwarsu babban rashi ne da zai daɗe ana jin raɗaɗinsa,” in ji sanarwar.

Kwamanda Idris ya roƙi Allah ya jiƙan su, ya ba su Aljannatul Firdausi, tare da roƙon Ubangiji ya ba iyalan da suka bari haƙurin jure wannan babban rashi.

A cewar sanarwar, Laftanar Kanar Abdullahi Bello (Rtd) kafin rasuwarsa shi ne kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Gombe, wanda aka sani da kishin ƙasa da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

By ukarofi