Na SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ƙaura Namoda da Birnin Magaji a Jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji ya yi Allah wadai da yunƙurin kace nace da wasu ‘yan jam’iyyar APC a jihar ke yi na ayi tsarin karɓa karɓar mulki kan wanda zai zama ɗan takarar gwamna a 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar ta APC a jihar.
Hon. Jaji ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a gidansa da ke Gusau yau Lahadi.
A cewarsa, batun tsarin karɓa karɓar mulki alama ce ta rauni a jam’iyyar ta APC a 2027.
“Ina ganin cewa tsarin karɓa karɓar mulki da wasu ‘yan APC ke yunƙurin kawowa ba abin a yarda da shi bane, amma na yi imanin cewa a zaɓo ɗan takaran da ya dace ne wanda zai iya kare muradun mutanen jihar, ba tare da la’akari da yankin da ya fito a jihar ba”. Ya ce
“Duk lokacin da kuka ji ana iron waɗannan batuwa na tsarin karɓa Karɓar mulki wata alama ce ta son zuciya, rauni ko kuma son kai a tsakanin mambobin jam’iyyar All Progressive Congress APC a jihar Zamfara musamman a zaɓen 2027 da ke tafe.” Hon. Jaji ya ce
A cewarsa, tun daga shekarar 1999, jihar Zamfara ba ta rungumi tsarin karɓa karɓar mulki ba, yana mai jaddada cewa yankin Zamfara ta Yamma ya samar da gwamnoni uku, yankin Zamfara ta Arewa ya samar da gwamna ɗaya yayin da gwamnan yanzu ya fito daga Zamfara ta tsakiya.
“Tun daga shekarar 1999, Sanata Ahmed Sani ya zama gwamna na tsawon shekaru takwas, Sanata Abdulaziz Yari ya shafe shekaru takwas sannan Matawalle ya shafe shekaru huɗu, dukkanin su daga yankin Zamfara ta Yamma suka fito.” Cewar Jaji
Ya ƙara da cewa Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi daga Zamfara ta Arewa ya shafe shekaru huɗu a matsayin gwamnan jihar Zamfara daga 2007 zuwa 2011, yayin da Gwamna Dauda Lawal shi ne gwamnan da ke kan mulki a yanzu daga Zamfara ta tsakiya.
“A nawa ra’ayin, ban yarda da wannan yunƙuri ba, amma ya kamata mu mayar da hankali kan haɗin kai, zaman lafiya da cigaban jam’iyyar mu, mu kuma zaɓi ɗan takarar da ya dace wanda zai zama gwamna na gaba a 2027 wanda ke da niyyar bunƙasa jihar”. Ya ƙara da cewa
Hon Aminu Sani Jaji ya ƙara da cewa jimillar ‘yan jam’iyyar PDP 2000 sun shiga jam’iyyar All Progressive Congress APC a ƙarƙashin ɓangaren sa, watau ƙungiyar Jaji Amana a jihar.
Hon. Jaji ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayanta a jihar da su ci gaba da haɗin kai, don samun nasara da ci gaban jam’iyyar a shekarar 2027.
A cewar sa, APC za ta iya yin nasara ne kawai a shekarar 2027 a jihar, idan ‘yan jam’iyyar suka haɗa kai suka kuma yi tafiya da murya ɗaya.
