Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da ƙarshen shekara ke gabatowa, rahotanni sun nuna cewa, yawancin manyan wuraren shaƙatawa da wuraren taro na alfarma a birnin Legas sun fara cika tun kafin lokacin hutun na Disamba, wanda ake yi wa laƙabi da ‘Detty December 2025’, ya iso.
Wannan na zuwa ne bayan Detty December 2024 ta kafa sabon tarihin shaƙatawa da nishaɗi a Nijeriya, inda ta zama ginshiƙi ga harkokin yawon buɗe ido da tattalin arzikin nishaɗi.
Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa Nijeriya ta samu kusan kashi 4% na tattalin arzikin GDP ɗinta daga ayyukan Detty December a bara. ƙididdiga ta nuna cewa wuraren raye-raye na dare a Legas sun tara sama da biliyan N111.5 daga yawon buɗe ido da nishaɗi a watan Disamba kaɗai.
Wani bincike ya nuna cewa yawancin manyan wuraren shaƙatawa da gidajen taro sun fara karɓar ajiyar kuci tun watan Satumba, yayin da wasu ke neman wuraren zama.
Ga jerin manyan wuraren shaƙatawa 20 mafi tsada a Legas da ake shirin mamaye su a wannan Detty December:
1. Beleza Beach Resort – miliyan N2.5 a dare.
2. Eko Convention Centre – miliyan N10 – miliyan N15 a dare.
3. Sencillo Lagos –miliyan N2.75.
4. Harour Point Event Centre – miliyan N8.25–N10.9.
5. Aƙualina Ilashe Private Beach House – miliyan N2.5–N4.6 a dare.
6. Sheraton Lagos Hotel (Moremi Hall) – miliyan N6.
7. La Campagne Tropicana Beach Resort – miliyan N1.9.
8. The Civic Centre – miliyan N5.95.
9. Havara Beach House – miliyan N1.26 a dare.
10. Landmark Event Centre – miliyan N5.
11. La Manga Beach Villa – miliyan N600,000 a dare.
12. The Monarch Event Centre, Lekki – miliyan N1.5–N13.
13. Yolo Beach Resort – miliyan N536,000 a dare.
14. Oriental Hotel, Lagos – miliyan N80,000–N7.2.
15. Salt Beach – N350,000– miliyan N3.5m a dare.
16. Ziba Beach Resort – miliyan N185,000 a dare.
17. Muson Centre – miliyan N90,700–N1.3.
18. Jara Beach Resort – miliyan N165,000–N225,000 a dare.
19. Simon’s Beach Resort, Ilashe – miliyan N4.5 a dare.
20. Balmoral Hall, Victoria Island – miliyan N500,000–N1.
Masana sun bayyana cewa Detty December ya wuce hutu kawai — ya zama wani biki ne na ƙara ƙarfin tattalin arziki da ke ƙarfafa yawon buɗe ido, nishaɗi, da bunƙasa ƙananan kasuwanni.
Tuni otel-otel, gidajen haya, da wuraren shaƙatawa ke baje kolin su, yayin da masu yawon buɗe ido da ’yan kasuwa daga gida da waje ke shirye-shiryen mamaye Lagos domin babban bikin ƙarshen shekara.
Idan bara ta kafa tarihin kuɗaɗe da nishaɗi, masana suna ganin Detty December ta bana ta 2025 za ta kasance mafi zafi, mafi ƙayatarwa, kuma mafi riba a tarihin Legas — kuma kamar yadda ake cewa, a Legas, Disamba ba ta jiran kowa.
