
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Alamun sulhu sun fara bayyana a Majalisar Dattawa yayin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya ta gayyaci Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio zuwa wajen ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a mazaɓarta, wanda za a yi a ranar Lahadi, a garin Ihimi na Jihar Kogi.
Akpabio ne da kansa ya karanta katin gayyatar musamman a zauren majalisa, ranar Laraba, kamar yadda NewsPointNigeria ta ruwaito.
Za a yi taron ne domin karrama Sanatar, wadda ta cika shekara biyu a Majalisar Dattawan da kuma buɗe ayyukan da aka kammala a mazaɓar Kogi ta Tsakiya.
Sanatar ta ce, za a haɗu ne gidanta da ke Fuloti na 101 a Layin Jimoh da ke Ihima a Okene, inda ta shawarci abokan aikinta da za su je ta jirgin sama da su sauka a garin Obajana kafin su ɗauki hanyar mota zuwa wajen taron.
Akpabio ya karɓi gayyatar da hannu biyu-biyu inda ya kuma nuna farin cikinsa tare da taya ta murna bisa nasarar da ta samu a matsayinta na sanata.
A watanni baya ne aka samu tsama tsakanin sanatocin biyu akan tsarin wajen zama a majalisar, lamarin da daga baya ya rikiɗe, inda Natasha ta zargi Akpabio da yunƙurin cin zarafinta da kuma dakatarwar watanni shida da aka mata daga majalisar.
