
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fannin lafiya a Nijeriya ya sake shiga halin rashin tabbas yayin da sama da likitoci 11,000 da ke ƙarƙashin ƙungiyar likitocin Nijeriya ta (NARD) suka shirya shiga yajin aiki a daren yau Asabar wayewar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa hakan zai shafi manyan cibiyoyin lafiya aƙalla guda 91 a Nijeriya ciki har da asibitocin koyarwa, manyan asibitoci da wasu asibitocin kuɗi, lamarin da ka iya shafar kula da marasa lafiya a faɗin ƙasar.
A watan hira ta wayar salula da manema labarai, Shugaban NARD, Dakta Muhammad Suleiman ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar tsayar da ayyuka sakamakon gazawar gwamnatin tarayya na biya musu buƙatu guda 19 da NARD ɗin ta gabatar mata duk da cewa kwanaki 30 na magiyar da gwamnatin ta yi sun ƙare.
Ya ce, Ma’aikatar Kuɗi ta yi ƙoƙarin magance wasu matsalolinsu, amma wannan ya magance wani ɓangare ne na buƙatun nasu ba kaso mai girma daga ciki, don haka sun yanke tafiya yajin aikin, inji shi.
Tun da jimawa likitocin suke koka wa gwamnati akan batutuwan da suka shafi walwalar ma’aikata a cibiyoyin kula da lafiya domin cigaba da tafiyar da al’amura bisa tsari da inganci.
