Sanata Natasha za ta fuskanci shari’a, inji Ma’aikatar Shari’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya tana da shari’a a gabanta, bisa tuhumar ɓatanci da laifin amfani da yanar gizo wajen yaɗa bayanan ƙarya da ake yi mata a kotunan Abuja biyu.

Ofishin Babban Lauyan Gwamnati (AGF) ya ƙaryata iƙirarin Sanatar cewa shari’ar da aka shigar da ita a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da kuma Kotun ƙoli ta Tarayya abin raina doka ne da kuma tsoma bakin siyasa.

A cewar ofishin AGF, an shigar da ƙarar ne bayan cikakken bincike da hukumomin tsaro suka gudanar, kuma an tabbatar da cewa akwai hujjoji na farko da ke nuna akwai abin da sanatar za ta amsa a gaban kotu.

Wannan matsaya ta Ma’aikatar Shari’a ta fito ne cikin takardar martani (counter-affidavit) da aka shigar domin kalubalantar roƙon da Sanata Natasha ta gabatar tana neman a soke shari’ar da hujjar cewa an yi mata hakan ne saboda siyasa.

Sanata Akpoti-Uduaghan tana fuskantar shari’o’i guda biyu daban: ɗaya a Babbar Kotun FCT kan laifin ɓatanci, ɗaya kuma a Kotun ƙoli ta Tarayya a kan laifin amfani da yanar gizo wajen yaɗa ƙarya.

Tuhumar ta samo asali ne daga zargin da Sanatar ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, cewa suna ƙulla makirci na kashe ta — abin da masu shigar da ƙarar suka ce ƙarya ce da ta ɓata musu suna.

A cikin takardar martanin gwamnati, ofishin AGF ya bayyana cewa shari’ar ba ta da nasaba da siyasa, domin an yi ta ne bisa tanade-tanaden Dokar Laifuffuka (Penal Code) da Dokar Laifuffukan Yanar Gizo (Cybercrimes Act).

“An shigar da tuhuma mai ƙunshe da abubuwa uku bayan cikakken bincike wanda ya tabbatar da akwai hujja ta farko da ke nuna cewa akwai abin da wadda ake tuhuma za ta kare kanta a kai,” inji takardar.

Haka kuma ta ƙara da cewa: “ƙarar da aka shigar ta fito ne daga cikakken bincike da Hukumar ‘Yan Sanda ta gudanar kan ƙorafe-ƙorafe da dukkan masu ruwa da tsaki a cikin al’amarin. Duk ƙorafe-ƙorafen da wadda ake tuhuma ta gabatar an bincike su sosai, kuma aka tabbatar da abin da ya dace kafin shigar da ƙara a kotu.”

Ofishin AGF ya jaddada cewa matakin da aka ɗauka “na cikin ikon da kundin tsarin mulki ya ba gwamnati domin tabbatar da adalci da kare martabar doka.”

A zaman kotu na baya-bayan nan a gaban Mai Shari’a Chizoba Oji na Babbar Kotun FCT, lauyan gwamnati, David Kaswe, ya sanar da kotu cewa an riga an shigar da takardar martani amma ba a kai wa wanda ake tuhuma ba.

Saboda haka, Kaswe ya nemi ɗan lokaci domin a mika takardar yadda doka ta tanada.

Lauyan Sanata Natasha, Ehiogie West-Idahosa (SAN), ya tabbatar cewa har yanzu abokiyar aikinsa ba ta samu takardar martanin gwamnati ba.

Daga nan ne Mai Shari’a Oji ta ɗage zaman zuwa 1 ga Disamba, domin sauraron ƙarar wucin gadi da Sanatar ta shigar tare da martanin da Ma’aikatar Shari’a ta gabatar.

By ukarofi