Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 116.4 ga ɗaliban Nijeriya sama da 624,000 da suka ci gajiyar Shirin Rancen ɗalibai na ƙasa (NELFUND) tun bayan ƙaddamar da tsarin neman rancen a ranar 24 ga Mayu, 2024.
Rahoton yau da kullum da hukumar ta wallafa a shafinta na ɗ (tsohon Twitter) ranar Talata, 28 ga Oktoba, ya nuna cewa hukumar ta karɓi 929,805 daga cikin waɗanda suka nemi rancen, inda 624,535 daga cikinsu suka amfana har zuwa yanzu.
Rahoton ya ƙara bayyana cewa, an samu 12,398 na sabbin ɗalibai da aka amince da su cikin wannan rana — ƙarin kashi 1.4 daga abin da aka samu a ranar da ta gabata.
A cewar hukumar, har zuwa 9 ga Oktoba, 2025, an biya biliyan N65.3 ga jami’o’i, kwalejoji da cibiyoyin fasaha 239 a matsayin kuɗin makaranta, sannan an sake raba biliyan N51.1 a matsayin tallafin rayuwa (upkeep allowance) ga ɗalibai. Hakan ya kai jimillar kuɗin da aka raba zuwa biliyan N116.4.
Tun da farko, hukumar ta sanar da buɗe sabuwar kafa ta neman rance domin shekarar karatu ta 2025/2026, wacce za ta gudana daga Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025 zuwa Asabar, 31 ga Janairu, 2026.
A cikin sanarwar da Daraktan Sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi, ya fitar ranar Talata, hukumar ta shawarci sabbin ɗalibai da su yi amfani da lambar admission ko lambar rajirtar JAMB maimakon lambar matric wajen cike fom ɗin neman rancen.
Hukumar NELFUND ta kasance hukuma wadda aka kafa domin aiwatar da Shirin Rancen ɗalibai na ƙasa, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kanta a watan Afrilu 2024.
