An kammala gasar ƙwallon ƙafa ta matasa ‘yan ƙasa da shekaru 18 (U-18) wadda aka sanya wa suna “President Bola Ahmed Tinubu U-18 Boys Football Tournament”, inda Jihar Kwara ta zama zakara bayan doke Jihar Bauchi a wasan ƙarshe da aka buga a filin wasa na Muhammadu Dikko Stadium, da ke cikin garin Katsina.
Wannan gasa wacce ta gudana ƙarƙashin jagorancin Ƙungiyar Wasannin Matasa ta Nijeriya (YSFON), ta tattaro ƙungiyoyi daga jihohi daban-daban na ƙasar nan domin baje kolin ƙwarewarsu a harkar ƙwallon ƙafa.
Bayan gasa mai cike da ƙwarewa da gasa, jihar Bauchi ta zo ta biyu, yayin da jihar Katsina U-18 ta samu matsayi na uku.
A wajen rufe gasar, an gudanar da bikin karramawa da bayar da kyaututtuka ga yan wasa da ƙungiyoyi tare da wasu jajirtattun mutane da suka bada gudummuwar su don ganin samun nasara a lokacin gasar.
Taron ya samu halartar manyan baƙi da dama ciki har da sakataren dindindin na Ma’aikatar Wasanni da Matasa, Hon. Muhammad Rabiu wanda ya wakilci Kwamishinan Ma’aikatar, Injiniya Surajo Yazeed Abukur, Hon. Aliyu Lawal Zakari wanda ya wakilcin Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Wali AA Rahamawa, Hon. Adidas, Hon. Jamilu Kayoki, Dr. Abdulrahman Aliyu, Hon. Abdulfatai Mashasha, da kuma wakilan ma’aikatun gwamnati da ƙungiyoyin matasa.
A nasa jawabin, wakilin Gwamnan jihar Katsina Hon Aliyu Lawal Zakari, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda gasar ta gudana cikin lumana da kuma yadda matasa suka nuna gwanintar su.
Ya kuma yaba da goyon bayan da gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta bayar wajen ganin an gudanar da gasar cikin nasara.
An rufe taron ne da bada kyaututtuka ga mafi kyau a tsaron raga, a matsayin ƙarfafa gwiwar matasa masu tasowa a fagen ƙwallon ƙafa.
Wasan da ya gudana a filin wasa na Muhammadu Dikko dake birnin Katsina, jihohi 15 suka shiga wasan.
