
Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Manufofin gwamnati, Daniel Bwala ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu da Shugaban Amurka, Donald Trump, na shirin ganawa a kwanaki masu zuwa.
Za a yi ganawar ne a kodai a Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock ko kuma Fadar White House ta Amurka.
An shirya haɗuwar ne domin tattauna muhimman batutuwan da tasowa bayan da Trump ya saka Nijeriya a jerin kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ke lura da su saboda zargin take haƙƙin ‘yancin addini da bada umarni ga Pentagon da ta duba yiwuwar kai hari kan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a ƙasar.
Saidai, Nijeriya ta musanta zargin inda ta ce ba daidai ba ne a ce hare-haren ƴan ya shafi wani addini guda a ƙasar.
A wani sako da Bwala ya wallafa a shafinsa na X, wanda kuma shi ne mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da sadarwar jama’a, ya ce shugabannin biyu na da manufar bai-ɗaya wajen yaƙi da ta’addanci.
Ya jaddada cewa Trump ya taɓa nuna goyon bayansa ga Nijeriya ta hanyar amincewa da sayar mata da makamai domin yaƙi da ‘yan ta’adda.
Amma a gefe guda kuma Shugaba Tinubu kuwa, a cewarsa, ya yi amfani da waɗannan kayan yadda suka dace tare da cimma manyan nasarori.
Bwala ya ƙara da cewa duk wata saɓani da ke akwai kan ko ‘yan ta’addan da ke Najeriya suna kai hare-hare ne kan Kiristoci kawai ko kuma kan mabambantan addinai, za a tattauna su kuma a warware su a lokacin da shugabannin biyu suka haɗu.
