Zargin kisan Kiristoci: Tinubu a ankare yake da barazanar Amurka, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu yana ankare da barazanar Shugaba Donald Trump na ɗaukar matakin soja a Nijeriya bisa zargin yi wa al’ummar Kiristoci kisan kiyashi.

A ƴan kwanakin nan ne Trump ya yi kalamai da dama bayan ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta, inda ya yi barazanar turo sojojin ƙasarsa matuƙar gwamnatin Nijeriya ta gaza dakatar da kisan gilla akan Kiristocin ƙasar.

Ya umarci sashen yaƙi da ya kasance cikin kimtsi domin yiwuwar fara atisaye a Nijeriya.

Da yake jawabi, Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, ya ce tuni Tinubu ya ɗauki matakan da suka dace musamman wajen yin garambawul ga jagororin tsaro da umarnin a samar da kayan aiki na zamani domin dabarun daƙile ayyukan ta’addanci.

A wani rubutu ta kafar X, Onanuga ya ce Shugaban ƙasar ya umurci sababbin jagororin tsaro da su fitar da dabarun daƙile ayyukan ta’addanci da ke cigaba da zama ƙalubale a sassan ƙasar.

Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth a wani rubutu ta X, ya ce “Ko dai Gwamnan Nijeriya ta tsare Kiristoci, ko mu kashe ƴan ta’addan musulunci da ke aikata waɗannan munanan ayyukan.”

Ya bayyana cewa, tuni suka fara shirye-shiryen kai farmaki ga ƙungiyoyin tsatstsauran ra’ayi da ake zargi da hannu a hare-haren.

By Babaji