
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani rahoto da jaridar PUNCH ta fitar ya bayyana yadda jami’an sojojin leƙen asiri suka bankaɗo kimanin Naira biliyan 11 a asusun wani kanal na soja da aka tsare bisa zargin juyin mulki da aka alaƙanta da wasu manyan sojoji a Nijeriya.
A cewar jaridar, majiyoyi na manyan jami’ai sun ce gano maƙudan kuɗaɗen na da alaƙa da tsararren jami’in, lamarin da ya ƙarfafa zargi akansa, wanda a baya aka tura shi aiki a yankin Neja-Delta.
Da ake bincike akansa game da kuɗaɗen, Kanal ɗin ya yi ikirarin cewa asalinsu na wani tsohon gwamna ne, wanda ya bayyana a matsayin abokin kasuwancinsa, yana mai tirjewa akan cewa kuɗaɗen na halastacciyar hulɗar kasuwanci ne.
Jaridar ta kuma gano cewa binciken na yanzu cigaba ne na wanda aka faro tun a watan Agustan 2024 a lokacin da wani bincike na sirri ya nuna cewa akwai wasu sojoji da ke kitsa makircin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa, akan haka ne Sashen Leƙen Asirin (DIA) na sojoji ya fara bin diddigin sadarwa, zirga-zirgar kuɗaɗe da alaƙoƙin waɗanda ake zargin watanni gabanin kama su.
Kazalika, binciken DIA akan al’amarin da rahotannin da take samu sun taimaka wajen rage zama a Abuja da yawan zuwa Legas ga Shugaba Bola Tinubu, kamar yadda majiyoyin suka bayyana.
