
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sababbin bayanai sun bayyana game da dabarun gwamnati wajen salon isar wa al’umma saƙo bayan bayyanar zargin kitsa juyin mulki a Nijeriya.
Wani rahoto da jaridar PRNigeria ta fitar ya bayyana cewa an samu shawarar shari’a ne jim-kaɗan bayan jami’an leƙen asiri na cikin gida da ke aiki a Hedikwatar Tsaro (DHQ) sun gano cewa hakan wani shiri ne na wasu jami’an sojoji da wasu fararen hula da suka ɗauki nauyinsu da nufin haddasa wa gwamnatin fitina.
Wani ƙwararre akan harkar shari’a da ke ba gwamnati shawara akan doka da lamuran tsaro ya yi gargaɗin cewa ayyana al’amarin a matsayin ‘juyin mulki’ abu ne da zai sa a fuskanci ƙalubale na shari’a, ɗabi’a da ayyuka.
Ya bayyana cewa, wajibi ne a ƙaurace wa amfani da kalmomi masu hatsari game da al’amarin har sai bincike ya kammala duba da barazanar da hakan ka iya haifar wa al’amarin shari’a.
Ya ƙara da cewa, masu bincike suna da buƙatar hujjoji masu ƙarfi kafin su yi wata sanarwa ga al’umma, yana mai cewa ayyana abin ta wata fuska ba tare da la’akari da sahihancinsu ba, za su iya samar wa aikin bincike tsaiko.
Jaridar ta kuma gano cewa, an kauce wa haka ne don kada a ba wa waɗanda aka haɗa baki da su a ciki da wajen sojoji damar tserewa.
